Gwamna AbdulRazaq Ya Hango Haɗari, Ya ba da Umarnin Rufe Makarantu a Jiharsa
- Gwamnatin Kwara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu kananan hukumomi hudu saboda karuwar tsaro a jihar
- Sanarwar da NUT ta karanta ta ce za a rufe makarantu a kananan hukumomi hudu ciki har da Irepodun, Ifelodun da Ekiti
- Gwamna AbdulRahman Abdulrazaq ya bukaci a kafa sansanin soji a yanin Eruku, garin da 'yan bindiga suka kai hari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Yanayin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a yankunan Kwara ta Kudu ya sa gwamnatin jihar ta rufe makarantu a kananan hukumomi hudu.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ba da umarnin a rufe dukkanin makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti.

Source: Twitter
An rufe makarantu a jihar Kwara
Gwamnati ta ba da wannan umarnin rufe makarantun ne ta hannun kungiyar malamai ta NUT reshen jihar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NUT na jihar, Yusuf Agboola, ya ce ma’aikatar ilimi da cigaban dan Adam ce ta bada umarnin rufe makarantun saboda barazanar tsaro da ake fuskanta.
Yusuf Agboola ya bukaci dukkanin makarantun da ke kananan hukumomin hudu su bi wannan umarni cikin gaggawa domin umarni ne kai tsaye daga gwamnatin jihar.
"An dauki wannan mataki na rufe makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun da Ekiti saboda matsalar taro da aka samu, da kokarin gwamnati na shawo kan matsalar."
- Yusuf Agboola.
Harin Eruku ya tayar da hankali a Kwara
Rufe makarantun ya biyo bayan mummunan harin da ya 'yan bindiga suka kai kauyen Eruku da ke cikin karamar hukumar Ekiti LGA.
Mun ruwaito cewa ’yan bindiga sun farmaki cocin CAC Oke-Isegun da yammacin Talata, suka kashe mutane sannan suka yi awon gaba da masu ibada akalla 35.
Wannan ya haifar da tashin hankali a yankin, tare da jawo matasa suka fito zanga-zanga da tare hanyar Ilorin-Kaba don nuna fushinsu a fili.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, bayan sun tare hanyar Ilorin-Kabba, Timothy Joshua, ya ce 'yan bindigar sun tafi da matarsa da jikarsa, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Source: Original
Gwamna ya nemi sansanin sojoji a Eruku
A ranar Laraba, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya ziyarci Eruku domin ganin halin da ake ciki bayan harin 'yan bindigar, in ji rahoton Channels TV.
Gwamna ya bukaci a kafa sansanin FOB na sojoji da kuma na 'yan sandan MOPOL a yankin domin murƙushe hare-haren ’yan bindiga.
Ya ce ya riga ya tattauna da GOC, watau shugaban rundunar soji ta 2 da kuma shugaban 'yan sanda IGP Kayode Egbetokun kan bukatar tsaurara tsaro a yankin.
Kwara: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hallaka akalla ‘yan sa-kai da mafarauta 15 a wata arangama da suka yi a jihar Kwara.
'Yan bindigan sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kai hari a garin Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
Wani mamba na kungiyar ‘yan sa-kai, wanda ya ce sunansa Ajetunmobi, ya tona cewa gwamnati na ɓoye gaskiya ta hanyar cewa an fatattaki maharan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

