Wata Sabuwa: Ana batun Daliban da Aka Sace, Majalisa Ta Dakatar da Ciyaman a Kebbi
- Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai, Hon. Muhammad Mahuta kan zargin rashin gaskiya
- Hakan dai ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamiti na musamman da Majalisar ta yi a zamanta na ranar Laraba a Birnin Kebbi
- Ana zargin ciyaman din da dauke wasu na'urorin raba wutar lantarki watau tiransufoma da nufin gyara amma ya fara yunkurin sayar da su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Yayin da ake jimamin sace dalibai mata daga makarantar sakandire ta Maga, Majalisar Dokokin jihar Kebbi ta waiwayi karamar hukumar Fakai.
Majalisar dokokin ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai, Hon. Muhammad Mahuta bisa zargin aikata manyan laifuffuka na rashin gaskiya da sakaci a wurin gudanar da aiki.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ce an yanke wannan hukunci ne bayan amincewa da rahoton kwamiti na musamman da Hon. Salihu Dangoje ya jagoranta, a zaman majalisar na ranar Laraba a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan
An saki sunayen dalibai 25 da aka sace a Kebbi bayan kalaman 'dan majalisar Amurka
Zargin da ake yi wa shugaban karamar hukumar
A cewar Hon. Dangoje yayin gabatar da rahoton, kwamitin ya binciki kwashe na'urorin lantarki na tiransufoma guda biyar da yunkurin sayar da su ba bisa ka’ida ba.
Bugu da kari, dan Majalisar ya ce sun yi bincike kan zargin ciyaman da bada gonakin gwamnati ba bisa doka ba tare da saba ka’ida a kwangilar gyaran Mahuta Dam.
Da yake kare kansa, Mahuta ya shaida wa kwamitin cewa an dauki tiransufoma ne domin gyarawa da izinin wani jami’in KEDCO, Malam Nasir, wanda bai bayyana gaban kwamitin ba.
Sai dai shugaban kwamitin, Dangoje ya bayyana cewa:
"A ranar 14 ga Nuwamba, shugaban karamar hukumar ya amince cewa an dauki tiransufoma din ne domin a sayar wa Alhaji Kabiru Dauda kowane kan N2.5m.”
Kwangilar gyaran Mahuta Dam
Shugaban karamar hukumar Fakai ya yi ikirarin cewa an ba kamfanin ZBCC kwangilar gyaran dam ɗin, amma Injiniyan ZBCC ya musanta hakan, ya ce hayar kayan aikinsu aka yi.
Babu wata shaida da ke nuna cewa an kammala bayar da kwangilar duk da cewa an biya kudin aikin, in ji rahoton Daily Post.
Kwamitin ya same shi da laifin rashin gaskiya, ladabi da sakaci a wajen aiki, saboda haka ya ba da shawarar a dakatar da Hon. Mahuta na tsawon watanni shida.

Source: Facebook
Majalisa ta dakatar da ciyaman a Kebbi
Hon. Muhammad Buhari (APC, Aliero) ne ya gabatar da kudirin dakatar da ciyaman ma karamar hukumar Fakai, wanda Nura Kangiwa (APC, Arewa) ya marawa baya.
Shugaban majalisar dokokin Kebbi, Muhammad Usman, ya bayyana cewa dakatarwar nan take ta fara aiki.
Mataimakin kakakin Majalisa ya kubuta
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Samaila Bagudu ya shaki iskar 'yanci bayan kwashe kwanaki a hannun 'yan bindiga.
An sace Samaila Bagudu ne a daren ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, 2025, a garinsa na Bagudu, hedikwatar karamar hukumar Bagudu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da ceto dan majalisar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
