Trump: Gwamnati Ta 'Dora Alhakin Karuwar Ta'addanci a Najeriya a kan Shugaban Amurka

Trump: Gwamnati Ta 'Dora Alhakin Karuwar Ta'addanci a Najeriya a kan Shugaban Amurka

  • Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce kalaman Donald Trump sun kara karfafa wasu kungiyoyin 'yan ta'adda a Najeriya
  • Kalamansa na zuwa bayan karuwa matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Neja, Kebbi da wasu sassan jihar Kano a 'yan kwanakin nan
  • Akume ya musanta batun cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi, yana cewa 'yan ta'addan ba sa bambance tsakanin Musulmi da Kirista

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya zargi kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da karfafawa ƴan ta'adda gwiwa.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Akume ya ce kaalaman Trump na cewa ana kashe kiristoci ya sa kungiyoyin kai hare-hare don daukar hankalin duniya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sanatan Amurka ya taso gwamnati a gaba kan sace dalibai a Kebbi

George Akumeya zargi kalaman Trump da zafafa matsalar tsaron Najeriya
Sakataren gwamnatin tarayya George Akume, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Yak Yak Angara/Donald J Trump
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito Akume ya tunatar da cewa tun kafin Trump ya zargi Najeriya da kisan gilla ga Kirista, aka rage tasirin ƴan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnati ya soki kalaman Trump

Vanguard ta wallafa cewa yadda Donald Trump ya sako Najeriya a gaba wajen ƙoƙarin ƙaƙaba mata laifin kisan kiristoci bai haifar da ɗa mai ido ba.

Ya ce:

“Kalamai daga Amurka sun ba wa wasu kungiyoyi damar kokarin shiga cikin labaran duniya ta hanyar kai hare-hare a wurare masu rauni.”

Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka zuwa Najeriya idan hare-haren kan Kirista ba su tsaya ba, tare da dakatar da duk tallafin Amurka idan gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Sai dai Akume ya musanta ikirarin cewa ana kisan kiristoci a Najeriya, yana mai cewa bincike ya nuna cewa ƴan ta'adda na kai hari kan coci da masallatai.

Gwamnatin tarayya ta nemi taimakon Amurka

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan sace daliban Kebbi da rashin tsaro a Kano

George Akume ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya ta riga ta kwato yankuna da dama tare da lalata tsarin Boko Haram da ISWAP.

Akume ya nemi agajin gwamnatin Amurka da makamai
George Akume, Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Yak Yak Angara/Donald J Trump
Source: Facebook

Ya jaddada cewa saboda haka, ba a bukatar tura dakarun kasashen waje su shigo cikin kasar nan da sunan yaki da yan ta'adda.

A cewarsa, abin da Najeriya ke bukata shi ne karin bayanan sirri, fasaha, da kayan aiki na zamani domin kara kakkabe ragowar ‘yan ta’adda.

Ya ce:

"Sojojin Najeriya kwararru ne, kuma sun yi nasarar gudanar da manyan ayyukan tsaro a fadin kasar. Ba mu bukatar sojojin waje; abin da muke bukata shi ne taimako na fasaha da bayanan sirri daga kasashen abokan hulda.”

Akume ya kuma jaddada cewa Najeriya kasa ce mai tsarin ba wa dukkanin addinai dama, kuma nade-naden gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun babu batun kisan kiristoci.

Tawagar Ribadu ta sauka a Amurka

A baya, mun wallafa cewa tawagar Najeriya, da Nuhu Ribadu ya jagoranta, ta isa Amurka domin bayyana matsayin Najeriya kan zargin wariya ga kiristocin kasar.

A ganawar da suka yi da dan majalisar Amurka, Riley Moore, Ribadu da sauran wakilai sun tattauna batun barazanar ta’addanci a Najeriya da yadda ta shafi kiristoci.

Kara karanta wannan

Annobar garkuwa da mutane ta sake kunno kai, an kwashe kusan mutum 150 a 'yan kwanaki

Moore ya kuma ce sun shirya aiki tare da Najeriya domin yaki da Boko Haram, ISWAP da wasu kungiyoyin ta’addanci da sassan kasar ke fuskanta a yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng