Sanata Maidoki Ya Yi Magana, An San Wurin da Yan Bindiga Suka Boye Daliban Kebbi
- Jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokarin dawo da daliban da aka sace daga makarantar Maga a Kebbi
- Lamarin dai na ci gaba da jawo hankalin manyan mutane a kasar nan, duk da gwamnati ta sha alwashin ceto 'yan matan cikin koshin lafiya
- Sanata Garba Musa Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta Kudu ya ce su na da masaniyar wurin da maharan suka boye daliban
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki, ya saki wasu bayanai da ke da alaka da kokarin ceto dalibai 'yan mata na makarantar Maga da aka sace.
Idan ba ku manta ba, yan bindiga sun kai farmaki makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke garin Maga, karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
An saki sunayen dalibai 25 da aka sace a Kebbi bayan kalaman 'dan majalisar Amurka

Source: Facebook
Rahoton Vanguard ya nuna cewa yayin wannan hari, yan bindigar sun sace dalibai mata guda 25, lamarin da ya ja hankalin 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano wurin da daliban Kebbi suke
Yayin da yake karin haske kan halin da ake ciki, Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki, ya bayyana cewa an san inda daliban Maga da aka sace suke.
Sanata Maidoki ya tabbatar da cewa har yanzun maharan ba su fitar da matan daga yankin ba, yana mai cewa nan da yan kwanaki za a ceto su cikin koshin lafiya.
Garba Maidoki ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake tattawa a shirin Politics Today na Channels Television, kwanaki bayan ’yan bindiga sun afka makarantar Maga, suka sace dalibai kusan 25.
Sanatan ya ce:
“Mun yi hasashen inda yaran suke, kuma muna da tabbacin cewa ba su fita daga yankin Kebbi ta Kudu ba. Akwai kyakkyawan fata cewa za su koma gida cikin kwana daya ko biyu.”
Matakan da gwamnatin tarayya ta dauka
Harin ya faru ne a ranar Litinin, inda mataimakin shugaban makarantar ya rasa ransa yayin yunkurin dakatar da ’yan bindigar.
Tun bayan lamarin, gwamnatin tarayya ta ba da umarni ga jami’an tsaro da su kubutar da daliban cikin gaggawa.
A ranar Laraba, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ziyarci al’ummar yankin bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Ya jaddada muhimmancin dawo da yaran lafiya kuma ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi.

Source: Twitter
Har ila yau, gwamnatin tarayya ta ce za ta yi amfani da dukkan karfin da take da shi domin dawo da daliban lafiya.
A cewar Sanata Garba Maidoki, har yanzu maharan ba su fita da daliban daga Kebbi ta Kudu ba, kuma suna fatan za a ceto su cikin yan kwanaki.
Sunayen daliban Kebbi da aka sace
A baya, mun kawo muku jerin sunayen dalibai mata 25 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin da suka kai makarantar Maga a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
'Hukumomi sun san za a kai hari makarantar Kebbi, suka ƙi ɗaukar mataki,' In ji Getso
Shugaban Karamar Hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, Hussaini Aliyu ne ya fitar da cikakken jerin sunayen 'yan matana bayan an fara zargin cewa duk kiristoci ne.
Ya kuma ayyana wannan zargi a matsayin mara tushe kuma abin tada fitina, musamman a lokacin da gwamnati ta mayar da hankali kan ceto yaran cikin koshin lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
