Wulakanta Naira: EFCC Ta Kama Malamar Coci bayan Bullar Bidiyo a Najeriya

Wulakanta Naira: EFCC Ta Kama Malamar Coci bayan Bullar Bidiyo a Najeriya

  • Wata fasto mai wa'azi a coci a jihar Delta, Archbishop Angel Oyeghe ta shiga hannun jami'an hukumar EFCC
  • Jami'an EFCC sun cafke malamar cocin ne bayan bullar wani bidiyo da aka ga mutane na watsa takardun Naira a kan saniya
  • Bayan bullar bidiyon wanda ya karade kafafen sada zumunta, EFCC ta gayyaci malamar cocin daga bisani kuma ta tsare ta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa watau EFCC ta kama Archbishop Angel Oyeghe, wata malamar coci a Warri, jihar Delta.

Jami'an EFCC sun cafke malamar, wacce ta kafa cocin Faith Healing Ministry da ke Warri, bisa zargin cin mutuncin takardun Naira, hada baki da wasu, da yiwuwar karbar kudin haram.

Archbishop Angel Oyeghe.
Hoton yadda aka yi watsi da Naira a coci da malamar da ke wa'azi a wurin a Delta Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafin ta na X yau Laraba, 19 ga watan Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

ISWAP: Kotu ta kama jagoran kungiyar 'yan ta'adda da laifi, ta yanke masa hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa EFCC ta kama malamar cocin?

An cafke Angel Oyeghe ne bayan wani faifan bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga mabiya cocin suna yi wa wata saniya mai rai liki da Naira a lokacin wani taron addini.

Faifan bidiyon ya kuma nuna malamar da ke jagorantar cocin a gefe tana kallo ba tare da hana ba.

EFCC ta ce binciken farko ya nuna cewa faston tana da alaka da lamarin, wanda ya sa hukumar ta gayyace ta, kuma daga bisani aka tsare ta.

Wane mataki EFCC ta dauka?

Hukumar yaki da rashawa ta kara da cewa tana bin diddigin sauran mutanen da suka shiga wajen watsa kudin domin a hukunta su daidai da abin da suka aikata.

A cewar EFCC, Fasto Oyeghe ta riga ta bayar da bayanai masu amfani ga jami'an da ke bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kashe mataimakin shugaban APC, 'yan sanda sun dauki mataki

Bidiyon da ya yadu sosai a kafofin sada zumunta, wanda EFCC ta wallafa tare da hotuna, ya nuna yadda masu ibada ke watsa takardun kudi a kan dabba.

Wane laifi aka aikata a cocin Oyeghe?

An tattaro cewa mahalarta cocin sun rika watsa kudi a kan saniyar ne yayin da ake gudanar da wasu addu'o'i a gaban malamar cocin.

Wannan na zuwa ne yayin da EFCC ta kara kai farmaki kan masu cin mutuncin kudin Najeriya watau Naira.

Zuwa yanzu dai EFCC ta kama tare da gurfanar da fitattun mutane kamar Cubana Chief Priest da Bobrisky a shekarar 2024 kan irin wannan laifi na watsa kudi a taruka.

Jami'an EFCC.
Hoton wasu jami'an hukumar EFCC a bakin aiki Hoto: EFCC Nigeria
Source: Twitter

EFCC ta fara neman Sylva ruwa a jallo

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta saka tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, a cikin jerin mutanen da ta ke nema ruwa a jallo.

Sylva, wanda ya rike kujerar karamin Ministan albarkatun man fetur a gwamnatin Marigayi Muhammadu Buhari, ya shiga cikin jerin mutane da EFCC take sa ido a kansu bisa zargin haɗin baki da karkatar da $14.8m.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

Hukumar EFCC ta nemi daukin hukumomin FBI ta Amurka, INTERPOL, da hukumar NCA ta Birtaniya don kamo Timipre Sylva.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262