Ana Jimamin Sace Dalibai a Kebbi, 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto

Ana Jimamin Sace Dalibai a Kebbi, 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto

  • 'Yan bindiga sun yi aika-aika bayan sun kai farmaki a wani kauye da ke cikin jihar Sokoto a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki kauyen ne a cikin dare inda suka yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Harin ya kara nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da cin tuwo a kwaryar mutanen Sokoto, wadda ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - ’Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki kauyen Tarah da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

'Yan bindigan wadanda suka kai harin a daren ranar Talata, sun yi garkuwa da mutum tara tare da jikkata wani mutum guda.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu da Sufeto Janar na 'yan sanda Hoto: @Ahmedaliyuskt, @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce an kai harin ne kwanaki kaɗan bayan an mayar da ’yan sa-kai na kauyen Tarah zuwa Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbe dan agajin Izalah, sun sace matarsa da jaririyar mako 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauke 'yan sa-kan ya bar kauyen ba tare da kariya ba a daidai lokacin da ake bukatar tsaro sosai.

Majiyoyi sun ce matasan yankin sun yi gaggawar taruwa inda suka fuskanci maharan, wanda hakan ya hana aukuwar barna mai muni a kauyen, rahoton ya zo a Daily Post.

'Yan bindiga na kai hare-hare

A baya-bayan nan, sace mutane da kashe-kashen al’umma a Arewacin Sokoto sun zama ruwan dare, inda 'yan bindiga ke farmakar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Wadannan hare-hare na baya-bayan nan sun sake bayyana bukatar da ake da ita wajen samun tsari na haɗin gwiwa domin kare al’ummomin da ke cikin hadari.

Lamarin ya kuma haifar da sabuwar damuwa game da yawaitar garkuwa da mutane da kuma kisa a jihar, musamman ganin cewa al’ummomi na ci gaba da fuskantar barazana duk da ayyukan tsaro da ake yi.

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

CAN: Dalibai da malamai 227 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a Jihar Neja

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce DPO na Sabon Birni bai kai rahoto ga hedkwata ba tukuna.

Sai dai ya tabbatar da cewa da zarar ya samu cikakken bayani game da lamarin, zai fitar da sanarwa ta musamman ga manema labarai.

'Yan bindiga sun yi aika-aika a jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dalhat Musa ya gayawa Legit Hausa cewa matsalar rashin tsaro sai dai addu'a kawai.

Mazaunin na jihar Sokoto ya bayyana cewa abin akwai ban tsoro yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a wasu sassan jihar.

"Lallai lamarin nan sai dai du'a'i kawai domin abin a wice duk inda ake tunani. Mutanen nan sun hana jama'a sakat."
"Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen wannan bala'in, Ya kuma yi mana maganin tsagerun mutanen nan."

- Dalhat Musa ​

Karanta wasu karin labaran kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

An kama wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya ta fito

'Yan bindiga sun kashe malamin addini

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan masu ibada a cikin wani coci da ke jihar Kwara.

'Yan bindigan sun bude wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka shiga garin Eruku da ke a cikin karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara.

Tsagerun kutsa cikin cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Isegun, inda suka harbe faston cocin tare da yin awon gaba da masu ibada da dama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng