Wasu Takardu daga Amurka Sun Nuna Wadanda Suka Zuga Trump Ya Kawo Hari Najeriya
- Wasu takardu daga ma'aikatar shari'a ta Amurka sun fallasa wadanda suka rinjayi Donald Trump har ya dauki mataki kan Najeriya
- Shugaba Trump dai ya dauki matakin sanya Najeriya a jerin kasashen da ake take hakkin addini, kuma ya yi barazanar turo sojojin Amurka
- Sai dai sababbin takardun da suka bulla kwanan nan sun nuna yadda 'yan fafutukar kafa kasar Biafra suka yada zargin kisan kiristoci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bayanai na ci gaba da fitowa kan wadanda suka ja ra'ayin gwamnatin Amurka har ta sanya Najeriya a jerin kasshen da ake take hakkin addini (CPC).
Idan ba ku manta ba, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi baranazar kawo farmaki Najeriya bisa zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Source: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa wasu sababbin takardun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da aka samu sun bayyana yadda kungiyoyin goyon bayan Biafra suka rinjayi Amurka.
Su waye suka ja ra'ayin Donald Trump?
Takardun sun nuna cewa wadannan kungiyoyi ne suka kitsa har suka jawo Amurka ta dauki wannan mataki kan Najeriya bisa zargi mara tushe watau kisan kiristoci.
An kuma gano cewa Shugaba Trump ya sanya Najeriya a jerin kasashen CPC, watau kasar da ake tauye 'yancin addini, saboda matsin lamba daga kungiyoyin 'yan kasashen waje mazauna Amurka.
Takardun sun bi diddigin abin zuwa United States of Biafra, wata gamayyar kungiya da ta ƙunshi Biafra Republic Government in Exile da Biafra De Facto Government in the Homeland.
Waɗannan kungiyoyi suna ƙarƙashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA) saboda manufarsu ita ce su rinjayi manufofin Amurka don cire kasar Biafra daga Najeriya.
Yadda 'yan Biafra suka rinjayi Amurka
A cewar takardun, kungiyoyin sun fi mayar da hankali kan ‘yan Amurka, musamman ƙungiyoyin siyasa masu ra’ayi irin na Shugaba Trump.

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka
Labarin da suke yadawa na nuna goyon bayan kafa Biafra a matsayin hanyar kare Kiristoci da kuma murkushe tasirin China a Afirka.
Manufofin wadannan kungiyoyin sun bayyana karara a cikin wata yarjejeniya da aka sanya hannu a Lahti, Finland a ranar 2 ga Disamba, 2024.
Mutanen da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya sun zargi Najeriya da kaddamar da “hari na kisan kare dangi” kan ‘yan Biafra da Kiristoci.
Sunayen mutum 3 da suka sa hannu
Daga cikin wadanda suka sanya hannu akwai Simon Ekpa, ɗan ƙasar Finland da ya bayyana kansa a matsayin Firaministan Biafra, wanda a halin yanzu yake zaman daurin shekaru shida a Finland kan laifukan ta'addanci da almundahana.
Sauran sun hada da Dr Ngozi Orabueze da Diane Emeh, dukkansu ‘yan ƙasar Amurka masu rike da manyan mukamai cikin ƙungiyar.
Takardun sun nuna cewa ƙungiyar na aiki ne domin samun karɓuwa a ƙasashen waje fiye da cikin Najeriya.

Source: Twitter
CAN ta yi maraba da matakin Trump
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa tabbas ana kisan kiyashi kan mambobinta a kasar bayan zargin da Amurka ta yi.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya ce abin takaici ne ganin Najeriya na shiga manyan jaridun duniya saboda mummunan yanayi.
Okoh ya ce suna maraba da shawarar Amurka na taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
