Kashim Shettima Ya Isa Kebbi, Ya Dauki Alkawura kan Daliban da Aka Sace

Kashim Shettima Ya Isa Kebbi, Ya Dauki Alkawura kan Daliban da Aka Sace

  • Ana ci gaba da jimami kan aika-aikar da 'yan bindiga suka yi ta sace wasu dalibai mata a kudancin jihar Kebbi
  • Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya kai ziyarar jajantawa al'ummar Kebbi kan iftila'in da ya auku
  • Kashim Shettima ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin cewa an kubutar da daliban

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya je jihar Kebbi bayan sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi.

Kashim Shettima ya bayyana sace daliban da aka yi a kauyen Maga, karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, a matsayin babbar masifa da za ta shafi kasa.

Kashim Shettima ya je jaje jihar Kebbi
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Kashim Shettima ya bayyana hakan ne yayin ziyayar jaje da ya je jihar Kebbi, a cewar sanarwar da hadiminsa ya sanya a shafin X.

Kara karanta wannan

An saki sunayen dalibai 25 da aka sace a Kebbi bayan kalaman 'dan majalisar Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Shettima ya ce kan sace dalibai?

Mataimakin shugaban kasar ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnatin tarayya za ta yi duk abin da ya dace domin ganin an ceto daliban cikin koshin lafiya.

“Raɗaɗin Kebbi raɗaɗin Najeriya ne.”

- Kashim Shettima

Ya kara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin damuwa sosai, kuma ya jajirce wajen ganin an kammala aikin ceton cikin nasara.

Shettima ya yi alkawarin cewa za a tura dukkan kayan aikin tsaro da ke hannun gwamnati domin tabbatar da cewa an dawo da yaran ba tare da wata cutarwa ba.

Haka kuma, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta tallafa wa iyalin mataimakin shugaban makarantar da ya rasa ransa yayin kare daliban.

“Za mu karrama iyalinsa, mu kula da su. Sadaukarwarsa ba za ta tafi a banza ba.”

- Kashim Shettima

Shettima ya yabawa jami'an tsaro

Mataimakin shugaban kasar ya jinjinawa jajircewar sojojin Najeriya, ’yan sanda, DSS da jami’an NSCDC kan aikin da suke yi domin kare rayukan jama’a.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Sanatan Amurka ya taso gwamnati a gaba kan sace dalibai a Kebbi

Shettima ya yaba musamman da rawar da marigayi Birgediya-Janar Musa Uba ya taka kafin rasuwarsa, yana mai cewa za a ci gaba da tunawa da sadaukarwar da ya yi.

Hakazalika, Shettima ya kuma yabawa gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, wanda ya kira a matsayin "cikakken jinin Arewa" tare da jinjinawa kan irin kokarin da yake yi a fannin tsaro.

Shettima ya gana da iyayen daliban da aka sace
Kashim Shettima tare da jami'an gwamnati yayin ziyarar da ya kai Kebbi Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

Ziyarar mataimakin shugaban kasa ta haɗa manyan jami’ai ciki har da ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, ministan jin kai, ministan harkokin mata, da shugaban APC na kasa.

A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya gode wa Shettima da Shugaba Tinubu bisa nuna kulawa, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin tarayya za ta shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Sanatan Amurka ya yi magana kan sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Jim Risch na kasar Amurka ya yi magana kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.

Sanata Jim Risch ya soki gwamnatin Najeriya kan yadda take bari 'yan ta'adda na sace daliban da ke zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

Hakazalika, ya bayyana cewa Amurka za ta dora alhaki kan gwamnatin Najeriya kan duk wata matsalar tsaro da aka samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng