ISWAP: Kotu Ta Kama Jagoran Kungiyar 'Yan Ta'adda da Laifi, Ta Yanke Masa Hukunci
- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama jagoran kungiyar ta'addaci ISWAP, Hussaini Isma'ila da hannu dumu-dumu a kai hare-hare Kano
- Hussaini Isma'ila, wanda aka fi sani da Mai Tangaran ya amsa laifuffuka hudu da DSS take tuhumarsa da aikatawa
- Kotun ta yanke masa hukuncin dauren shekaru 20 a gidan gyaran hali kuma ta ce za a fara lissafi ne tun daga ranar da aka kama shi a 2017
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Daya daga cikin jagororin kungiyar ta'addanci a Najeriya, ISWAP, Hussaini Ismaila ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su a gaban kotu.
Hakan dai ya biyo bayan shafe tsawon lokaci ana shari'a bayan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke shi, sannan ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya a Abuja.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kotun ta samu jagoran ISWAP din da laifin ta’addanci kuma ta yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran ISWAP ya amsa laifinsa
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin bayan Ismaila, wanda aka fi sani da Mai Tangaran, ya amsa laifuffukan tuhume-tuhume hudu na ta’addanci da hukumar DSS ta shigar a kansa.
Masu shigar da kara sun bayyana cewa Ismaila ya jagoranci kai hare-hare da dama ciki har da wanda aka kai Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Bompai, Jihar Kano a 2017.
Haka zalika Mai Tangaran shi ya jagoranci kai hare-hare kan ‘yan sandan MOPOL a titin Kabuga, Pharm Centre da ofishin ‘yan sanda na Angwa Uku duk a cikin Kano, da dai sauransu.
Yadda DSS ta gurfanar da Mai Tangaran
Bayan kama shi a ranar 31 ga Agusta, 2017, a Kauyen Tsamiya Babba, Karamar Hukumar Gezawa, Kano, an gurfanar da shi kan tuhume-tuhume hudu da suka danganci dokar hana ta’addanci ta 2013.
Shari’ar ta ɗauki lokaci saboda daukaka kara da kuma sarkakiya, har zuwa lokacin da ya furta da bakinsa kuma ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba tare da tilastawa ba.
Hukuncin da aka yanke wa jagoran ISWAP
A hukuncin, Mai shari’a Nwite ya same shi da laifi kan dukkan tuhume-tuhumen hudu, tare da yanke masa daurin shekararu 15 a tuhuma da farko da shekaru 20 a sauran tuhume-tuhumen.
Sai dai Alkalin ya ce hukuncin zai gudana a lokaci guda ma'ana dan ta'addan zai yi shekaru 20 a gidan yari, kuma za a fara lissafi daga ranar da aka kama shi, 31 ga Agusta, 2017, cewar The Nation.

Source: Twitter
DSS ta kai karar mai neman juyin mulki
A wani labarin, kun ji cewa hukumar DSS ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 27, Innocent Onukwume, bisa zargin yin kira da a yi juyin mulki a Najeriya.
Hukumar DSS ta shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a watan Oktoba na wannan shekarar da muke ciki watau 2025.
DSS ta bayyana cewa Onukwume ya wallafa sakonni a shafinsa na kafar sada zumunta da ke kira ga kifar da gwamnatin dimokuradiyya a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

