Babbar Magana: Sanatan Amurka Ya Taso Gwamnati a Gaba kan Sace Dalibai a Kebbi
- Daya daga sanatocin majalisar dattawan Amurka, ya yi tsokaci kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi
- Sanata Jim Risch ya soki gwamnatin Najeriya kan yadda take bari ana sace 'yan kasarta masu rauni domin karbar kudin fansa
- Ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnaton tarayya domin bada kariya ga mutanen da ke da rauni a al'umma
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Amurka - Sanata Jim Risch na jihar Idaho, daga Amurka, ya yi magana kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.
Sanata Jim Risch ya soki Najeriya kan sace daliban mata da aka yi, yana mai cewa tsawon lokaci kasar ta gaza wajen kare ɗalibanta daga hare-haren mayakan jihadi da kuma kungiyoyin ’yan ta’adda.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan
'Ba 25 ba ne,' Gwamnati ta fadi hakikanin adadin dalibai mata da aka sace a Kebbi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace dalibai a Kebbi
Sanarwar ta fito ne jim kaɗan bayan harin da aka kai GGSS Maga a jihar Kebbi, inda ’yan bindiga suka kashe mataimakin shugaban makarantar tare da sace dalibai 25, lamarin da ya jawo fushin jama’a a cikin gida da kasashen waje.
Mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku ya rasa ransa yayin harin, yayin da wani mai gadi, Ali Shehu, ya samu raunin harbin bindiga a hannunsa na dama.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Kebbi, Nafi’u Abubakar Kotarkoshi, ya ce maharan sun zo ne dauke da manyan makamai.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa an yi garkuwa da ɗaliban duk da cewa an samu bayanan sirri game da yiwuwar harin ’yan bindiga tun kafin faruwar lamarin.
Me Sanatan Amurka ya ce kan lamarin?
Sanata Risch ya bayyana cewa daliban makaranta, musamman ’yan mata sun zama wadanda ake kai wa harin don yin bautar dole, tilasta canza addini ko kuma neman kuɗin fansa, jaridar Vanguard ta jawi rahoton.
Ya kara da cewa Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan kare mutanen da suka fi rauni a cikin al’umma.
Hakazalika ya jaddada cewa za a dora alhaki a wuyan Najeriya kan duk wani gibin tsaro da aka samu.

Source: Twitter
"Najeriya ta daɗe tana gazawa wajen kare mutanenta daga sace-sacen masu da'awar jihadi da na miyagu, kuma ba wani canji mai ma’ana da aka samu.”
"Yayin da Amurka ke tattauna wa da gwamnatin Najeriya game da kariyar mutanen da suka fi rauni, za mu ci gaba dora alhakin komai a kansu."
- Sanata Jim Risch
Shugaba Tinubu ya dage tafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dage tafiyar da ya shirya yi zuwa kasashen Afrika ta Kudu da Angola.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya dage tafiyar ne domin karbar rahoton tsaro kan sace dalibai mata a Kebbi da harin 'yan bindiga a wata cocin jihar Kwara.
Hakazalika ya kuma bada umarnin tura karin jami'an tsaro zuwa karamar hukumar da 'yan bindiga suka kai hari a Kwara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
