Tinubu Ya Fasa Tafiya zuwa Kasashen Waje bayan Abubuwa Sun Rikice a Najeriya

Tinubu Ya Fasa Tafiya zuwa Kasashen Waje bayan Abubuwa Sun Rikice a Najeriya

  • Mai girma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dage tafiyar da ya yi niyyar yi zuwa kasashen Afrika ta Kudu da Angola
  • Dagewar na zuwa ne bayan shugaban kasan ya shirya barin babban birnin tarayya Abuja domin tafiya zuwa kasashen guda
  • A cikin sanarwa da hadimin shugaban ya fitar, ya bayyana cewa Tinubu zai jira rahoto daga wajen Kashim Shettima da hukumomin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dage tafiyar da ya yi shirin yi zuwa wasu kasashen waje.

Mai girma Tinubu ya dage tafiyar ne zuwa birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu da birnin Luanda na kasar Angola.

Shugaba Tinubu ya dage tafiyar da ya yi niyyar yi
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Hadimin shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.

Tun da farko, an tsara Shugaba Tinubu zai bar Abuja yau domin halartar taron shugabannin kasashen G20 karo na 20 a Afrika ta Kudu, sannan daga nan ya wuce birnin Luanda domin halartar taron AU-EU karo na bakwai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi sauyi a gwamnati, ya ba ɗanuwan marigayi Shehu Shagari muƙami

Tinubu ya fasa zuwa Afrika ta Kudu

A cewar Dada Olusegun, Shugaba Tinubu ya dage tafiyar ne domin ya jira karin rahotannin tsaro game da ’yan matan makarantar Kebbi da aka yi garkuwa da su da kuma harin da aka kai wa masu ibada na cocin Christ Apostolic Church a Eruku, jihar Kwara.

Hakazalika, ya bayyana cewa shugaban kasan ya umurci a tura karin jami'an tsaro zuwa Eruku sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai.

"A martanin bukatar da gwamnan Kwara ya gabatar, Shugaba Tinubu ya umurci karin jami’an tsaro su tafi Eruku da dukkan yankin karamar hukumar Ekiti ta jihar, tare da umartar ’yan sanda su bi diddigin ’yan bindigan da suka kai harin kan masu ibada."

- Dada Olusegun

Me yasa Tinubu ya dage tafiyar?

Dada Olusegun ya ce Shugaba Tinubu ya dage tafiyar ne saboda hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihohin Kwara da Kebbi.

"Sakamakon damuwa da matsalolin tsaro da aka samu a jihar Kebbi da kuma harin da ’yan bindiga suka kai wa masu ibada a cocin Christ Apostolic Church, Eruku ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya yanke shawarar dakatar da tafiyarsa."

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

"Yanzu haka yana jiran rahoton mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa Kebbi a madadinsa, da kuma rahotannin ’yan sanda da hukumar DSS kan harin da ya faru a Kwara."
"Shugaba Tinubu ya sake jaddada umarninsa ga hukumomin tsaro da su yi duk abin da ya kamata domin ceto ’yan mata 24 da ’yan bindiga suka sace, tare da dawo da su gida cikin koshin lafiya."

- Dada Olusegun

Shugaba Tinubu na jiran rahoton tsaro
Mai girma Bola Tinubu a cikin ofis Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Matawalle ya fadi sakon Tinubu ga sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya kai ziyara a hedkwatar rundunar Operation Fansan Yamma da ke jihar Zamfara.

Matawalle ya gayawa dakarun sojoji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba su tabbacin ba su dukkanin goyon bayan da suke bukata wajen yaki da matsalar tsaro.

Ministan ya kuma ba su tabbacin cewa sadaukarwar da suke yi domin ganin tsaro ya inganta a kasar nan, ba za ta tafi a banza ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng