Duniya Labari: Sanata Mai Ci a Najeriya Ya Rasu a Birtaniya yayin Jinya

Duniya Labari: Sanata Mai Ci a Najeriya Ya Rasu a Birtaniya yayin Jinya

  • Najeriya ta yi babban rashi bayan da aka sanar da mutuwar sanata mai ci wanda ya bar duniya bayan fama da jinya
  • Sanata Okey Ezea daga Enugu ta Arewa ya rasu a Birtaniya lamarin da ya girgiza jam’iyyar LP da mutanen yankinsa
  • Ezea shi ne ɗan majalisa guda kaɗai da ya ragewa LP daga Enugu, abin da ya sa rashin nasa ya fi ɗaga hankalin jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu - Majalisar dattawa ta shiga jimami bayan sanar da mutuwar daya daga cikin mambobinta a kasar Birtaniya.

An tabbatar da cewa Sanata Okey Ezea, wanda yake wakiltar Enugu ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya rasu a Birtaniya yayin da yake karɓar magani.

Najeriya ta yi rashin Sanata a Birtaniya
Taswirar jihar Enugu da marigayi sanatan ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Sanata a Najeriya ya rasu a Birtaniya

Leadership ta ce Ezea ɗan jam’iyyar LP ne, kuma shi kaɗai ne ya rage daga Enugu a majalisa, wanda hakan ya sa labarin ya tada hankali.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa rasuwar ta faru ne a ranar Talata 18 ga watan Nuwambar 2025, bayan ya yi doguwar jinya, lamarin da ya girgiza ’yan siyasa da sauran jama’a.

Shahararren mai shirye-shiryen rediyo, Chijinkem Ugwuanyi, ya bayyana rasuwar a Facebook, yana mai cewa “Sanata Okey Ezea ya rasu…”.

Mutanen Enugu ta Arewa da magoya baya sun bayyana alhini, saboda sanatan yana daga cikin fitattun jiga-jigan da suka tsaya da jam’iyyar LP.

Sanata Orji Kalu ya yi jimamin mutuwar takwaransa a London
Marigayi Sanata Okey Ezea wanda ya rasu a Birtaniya. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu.
Source: Facebook

Natasha ta yi jimamin mutuwar Okey Ezea

Abokan aikinsa da dama sun tura sakon ta'aziyya ga iyalansa, abokan arziki da kuma al'ummar jihar Enugu kan babban rashin da aka yi.

Daga cikin su akwai Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan wacce ta nuna damuwa game da rashin tare da yi masa addu'a ta musamman a Facebook.

Natasha ta bayyana cewa ba za ta manta da irin addu'o'insa ba lokacin da take cikin wani yanayi inda ta ce za ta yi kewarsa sosai.

Kara karanta wannan

Masu Umrah sun kone kurmus da motar su ta yi karo da tankar mai a Madina

Sanata Kalu ya fadi alakarsa da marigayin

Har ila yau, Sanata Orji Uzor Kalu daga jihar Abia ya bayyana takaicinsa kan rashin sanata Ezea wanda ya bar duniya bayan fama da jinya.

Kalu ya ce marigayin ya wuce ya rika shi da abokin aiki a majalisa, ya ce Ezea kamar abokinsa ya ke wanda ya kasance mutum mai son mutane.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya, kan-kan da kai da kuma son addini saboda ya sanshi sosai a cocin da suke zuwa ibadah.

Sanata ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook inda ya yi masa addu'a tare da tabbatar da cewa sun yi rashin mutumin kirki a majalisa.

Sanata daga jihar Anambra ya rasu

A baya, mun ba ku labarin cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya kwanaki kadan bayan barin Najeriya.

Marigayin dan jam'iyyar APC da ke wakiltar Anambra ta Kudu ya rasu ne a dakin otal da ke birnin Landan a kasar Burtaniya.

Kara karanta wannan

Mansur Sokoto ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe shugaban MSSN a Kebbi

Ubah kafin rasuwarsa, ya ba da gudunmawar N71m ga APC a jiharsa a kokarin kwace mulkin jam'iyyar APGA daga hannun Charles Soludo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.