'Ba 25 ba ne,' Gwamnati Ta Fadi Hakikanin Adadin Dalibai Mata da Aka Sace a Kebbi
- Adadin daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar sakandaren gwamnati ta mata da ke Maga, jihar Kebbi ya haura 25
- Kwamishinar ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Dr. Halima Muhammad Bande ta bayyana cewa dalibai 26 aka sace
- Wani mazaunin garin kuma dan uwa ga mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, Abubakar Dabai ya fadi halin da suke ciki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta warware rudanin da aka samu game da yawan daliban da aka sace a makarantar kwana ta mata ta GCGSS, Maga, jihar Kebbi.
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki makarantar da safiyar Litinin, suka kashe mataimakin shugaba tare da sace dalibai.

Source: Twitter
Adadin dalibai mata da aka sace a Kebbi
Sai dai, kwamishinar ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Dr. Halima Muhammad Bande ta ce adadin daliban da aka sace sun haura 25, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Halima Muhammad Bande ta bayyana cewa dalibai mata 26 ne aka sace, sabanin 25 da kafafen watsa labarai ke rahotowa bayan harin.
Kwamishinar ta bayyana cewa:
"Biyu daga cikinsu, Salmat da Hauwa sun kubuto daga hannun 'yan ta'addan. Yanzu muna da ragowar dalibai 24 a hannunsu."
Ta ce bayyana gaskiyar yawan daliban da aka sace ya zama wajibi saboda an samu kafofin labarai da suke rahoto bayanai game da lamarin da ba haka ba ne.
Gwamnati ta dauki mataki kan sace dalibai
Dr. Halima Muhammad Bande ta ce Gwamna Nasir Idris da gwamnatin tarayya sun dauki dukkanin matakan da suka dace.
Kwamishinar ta ce daga cikin matakan da aka dauka akwai tura jami'an tsaro zuwa dazuzzuka domin ceto daliban da kama maharan.
"Mu ci gaba da yi masu addua. Ba mu san inda suke ba, kuma ba mu san me suke yi wa 'yan matan nan ba, amma Allah zai dawo mana da su cikin aminci."
- Dr. Halima Muhammad Bande.

Source: Original
Ana zama dari-dari bayan sace dalibai
Tun bayan faruwar lamarin, an rahoto cewa ana zaman dari-dari a garin Maga, inda da yawan mutane suke zaune a gidajensu.
Wani mazaunin garin kuma dan uwa ga mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, Abubakar Dabai ya bayyana cewa har yanzu suna cikin tashin hankali.
"Kowa yana a firgice. Mun ma kasa zuwa gonakinmu, saboda ba mu san me zai faru da mu ba a nan gaba. Amma gwamna ya zo jiya ya ba mu tabbacin za a kare mu.
"Ya fada mana cewa gwamnati za ta turo karin jami'an tsaro don nemo yaran. Mun dora yakini a kansa. Za mu ci gaba da rokon Allah ya dawo mana da su lafiya."
- Abubakar Dabai.
Halin da Maga ke ciki bayan sace dalibai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, iyayen daliban da aka sace a makarantar kwana ta mata da ke Maga, Kebbi, sun mamaye harabar makarantar.
Wasu daga cikin iyayen, sun bayyana cewa ba za su iya komawa gida ba har sai 'ya'yansu sun dawo gare su cikin aminci.
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, da 'yan bindiga suka kashe a harin, ta fadi yadda maharan suka kashe mutane biyu, ciki har da mijinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


