Tinubu Ya Yi Sauyi a Gwamnati, Ya Ba Ɗanuwan Marigayi Shehu Shagari Muƙami

Tinubu Ya Yi Sauyi a Gwamnati, Ya Ba Ɗanuwan Marigayi Shehu Shagari Muƙami

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Musa Adar a matsayin shugaban hukumar NEITI inda zai canji Ogbonnaya Orji
  • Tinubu ya ba shi mukamin ne bayan raba shi da kujerar shugabancin NIWA, tare da nada tsohon ministan albarkatun ruwa, Mukhtar Shagari
  • Shugaban kasa ya bukaci sababbin shugabannin da ya nada da su nuna kishin kasa tare da sauke nauyin da aka dora masu ta hanyar aiki yadda ya dace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada Musa Adar zuwa sabon matsayi a matsayin shugaban hukumar tabbatar da adalci a bangaren ma'adanai (NEITI).

Musa Adar zai maye gurbin Ogbonnaya Orji wanda ya rike kujerar tun daga 2021 domin ya ci gaba da kawo sauyi bisa tsarin mulkin Tinubu.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

Shugaba Tinubu ya yi sababbin nade-nade
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan na kunshe ne cikin sanarwar da darektan yada labarai na na ofishin Sakataran Gwamnatin Tarayya (OSGF), Segun Imohiosen, ya fitar a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi sababbin nade-nade

Politics Nigeria ta wallafa cewa Adar ya bar tsohon matsayinsa na Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIWA) domin kula da NEITI.

Haka kuma gwamnati ta nada tsohon Ministan Albarkatun Ruwa, Mukhtar Shagari, a matsayin sabon shugaban hukumar NIWA.

A cikin sanarwar da ya fitar, Imohiosen ya ce dukkannin sauye-sauyen da nadin sababbin jami’an sun fara aiki nan take ba tare da wani jinkiri ba.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa an zabi sababbin jami’an ne bisa cancanta da bukatar kara habaka gudanarwa a hukumomin gwamnati.

Ya bukace su da su yi aiki da kishin kasa, tare da amfani da gogewarsu wajen hidima ga al’umma a hukumomin da aka damka musu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai nada jakadu bayan DSS ta mika sunayen mutanen da ta tantance

Gwamnati ta kare nade-naden gwamnati

Sauye-sauyen Tinubu sun sake jawo tattaunawa kan yadda gwamnatin tarayya ke rarraba manyan mukamai.

Gwamnatin tarayya ta ce tana nade-nade bisa tsarin doka
Shugaban kasa, Bola Tinubu yana rubutu a cikin wata takarda Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A watan Oktoba, Kayode Oladele, mukaddashin shugaban hukumar daidaito ta kasa (FCC), ya ce dukkannin nade-naden da gwamnatin Tinubu ke yi na bisa tsarin mulki.

A cewar Oladele, kididdigar FCC ta nuna cewa yankin Arewa ke rike da 56.3% na manyan mukaman shugabanci na tarayya, yayin da Kudu ke da kashi 43.7%.

Ya ce wannan na nuna cewa gwamnati na kokarin samar da daidaito tare da tabbatar da cewa kowane yanki ya samu wakilci yadda ya dace.

Shugaba Tinubu ya yi nade-nade

A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗe-naɗe a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin karfafa aikin hukumar kafin babban zaben 2027.

Sanarwar da Fadar Shugaban kasa ta fitar ta bayyana cewa an nada Abdulrazak Yusuf Tukur a matsayin sabon kwamishinan hukumar da zai kula da shiyyar Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

A cewar fadar shugaban ƙasa, an zaɓi Abdulrazak Yusuf Tukur ne bisa la’akari da kwarewar sa da cancanta wajen aiki a manyan hukumomin gwamnati, kuma ana san rai zai yi aiki tukuru.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng