Kusa a APC Ya Ji Kunya, Ya Nemi Afuwar Majalisa kan Zargin Cin Hancin N14bn

Kusa a APC Ya Ji Kunya, Ya Nemi Afuwar Majalisa kan Zargin Cin Hancin N14bn

  • Jigon APC ya rusuna a gaban majalisar dattawa inda ya nemi afuwa game da zargin su da karbar cin hancin
  • Alwan Hassan wanda ya fito daga Kano, ya janye ikirarin cewa sanatoci sun karɓi dala miliyan 10 don jinkirta tantance Abdullahi Ramat
  • Ya bayyana cewa ya dogara da maganganun da ya ji wajen bibiyar dalilin jinkirin tabbatar da Ramat a NERC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigon jam'iyyar APC, Alwan Hassan ya nemi afuwa a gaban majalisa bayan zargin mambanta da karbar cin hanci.

Alwan Hassan wanda ya zargi sanatoci da karɓar dala miliyan 10 don jinkirta tabbatar da Abdullahi Ramat a shugabancin NERC, ya janye wannan kalamansa.

Jigon APC a Kano ya nemi afuwar majalisa kan zargin cin hanci
Dandazon masu zanga-zanga game da kin tantance Abdullahi Ramat a matsayin shugaban NERC. Hoto: Hon. Alwan Hassan/Barau I Jibrin.
Source: Twitter

'Dan APC ya nemi afuwar majalisa kan sharri

Alwan Hassan wanda ɗan siyasa ne daga Kano, ya ce ya yi wannan magana ne bisa bayanan da ya ji yayin neman fahimtar dalilin da yasa Majalisar ta jinkirta tabbatarwar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

'Yadda mutuwar Gaddafi a Libya ke ci gaba da zama barazana ga Najeriya'

Ya nemi afuwa ga shugabancin Majalisar Dattawa a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce bayan bincike ya gane cewa zargin ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, ya yi maganganun da ba su dace ba game da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Mataimakinsa Barau Jibrin, wanda yanzu ya gane kuskure ne.

Ya kara da cewa zargin da ya ambata ya fito ne daga tattaunawar da ya yi da mutane, amma daga baya ya fahimci cewa ba daidai bane ko kadan.

Alwan ya ce ya janye zargin gaba ɗaya ba tare da wata shakka ba, tare da neman afuwa ga Majalisa da shugabanninta kan duk wani rashin gaskiya da aka danganta musu.

Dan APC ya ba majalisa hakuri kan yi musu sharri
Mambobin majalisar dokoki yayin zama a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Zargin da ake yiwa kusan na APC

Janyewarsa ta biyo bayan kama shi da kuma tsare shi da ’yan sanda suka yi kan wannan zargi, duk da cewa ba a bayyana tsawon lokacin tsarewar ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

An ce manyan mutane sun shiga tsakani suka taimaka wajen ganin an sake shi, bayan ya shaida wa manema labarai makonni da suka gabata cewa an ba sanatoci cin hanci.

Ramat dai ya kwashe sama da wata guda yana jiran Majalisa ta tabbatar da shi, bayan Shugaba Bola Tinubu ya mika sunansa don duba cancantarsa.

Rokon da Alwan Hassan ya yi ga majalisa

Bayan neman afuwa, Hassan ya sake roƙon Majalisar Dattawa da ta amince da Ramat, yana mai jaddada cewa yana da kwarewa mai sosai ga tsarin makamashin kasa.

Ya ce yana girmama rawar da Majalisar ke takawa, kuma wannan lamari ya koya masa muhimmancin bin ka’ida da mutunta cibiyoyin dimokiradiyya.

Matashin ya ce yana da kishin gaskiya, amma hakan ya koya masa cewa ya kamata duk wani yunkuri ya kasance cikin ladabi da bin doka.

An bukaci karin wata jiha a Najeriya

Kun ji cewa kungiyar Aba State Movement (ASM) ta bukaci majalisar dokoki ta tabbatar da Aba a matsayin jiha ta shida a Kudu maso Gabas.

Ta ce an dade ana gabatar da bukatar ga majalisar kasa tun daga 1952, tare da cewa Aba ta cika dukkan sharudda a tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

Shugaban kungiyar ya kara da cewa Ohanaeze Ndigbo ta nuna goyon bayan mayar da Aba zuwa jiha ta shida a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.