Abduljabbar: Sowore da Lauyoyi Sun Dura a Kurkuku, An Soki Ganduje kan Lamarin

Abduljabbar: Sowore da Lauyoyi Sun Dura a Kurkuku, An Soki Ganduje kan Lamarin

  • Wata tawaga da Omoyele Sowore da Barista Hamza Dantani suka jagoranta ta ziyarci Sheikh Abduljabbar Nasiru a gidan yari a Kuje
  • Lauyoyin sun nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamin a gidan kaso da zargin an siyasantar da shari’arsa da zargin saka hannun Abdullahi Ganduje
  • Sun ce wasu na kusa da malamin sun hada kai da manyan ’yan siyasa da malaman addini don tabbatar da hukuncin, duk da rashin adalcin shari’ar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - 'Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya sake bayyana damuwa kan ci gaba da tsare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yari.

Sowore ya jagoranci wata tawaga da ta hada da Barista Hamza Nuhu Dantani domin kai ziyara gidan gyaran hali na Kuje.

Sowore ya ziyarci Abduljabbar a kurkuku
Sowore da Dantani yayin ziyartar Abduljabbar a gidan yari. Hoto: Omoyele Sowore.
Source: Facebook

Sowore da lauyoyi sun ziyarci Abduljabbar

Kara karanta wannan

Masu Umrah sun kone kurmus da motar su ta yi karo da tankar mai a Madina

Hakan na cikin wani rubutu da Sowore ya yi wanda ya wallafa a shafin Facebook a jiya Talata 18 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sowore ya ce sun kai ziyarar ce shi da Nuhu Dantani domin ci gaba da bibiyar lamarin inda suke zargin akwai siyasa a lamarin hukuncin da aka yiwa malamin.

A cikin rubutunsa, Sowore ya ce:

"A yau, tare da Barista Hamza Nuhu Dantani, mun kai ziyara gidan yari na Kuje domin ganin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa.
"Mun bayyana cewa shari’ar tasa ta kasance mai cike da siyasa, karkashin tsohon gwamna Ganduje, tare da cin amanar da wasu suka yi masa."
Sowore ya zargi Ganduje kan lamarin Abduljabbar
Malam Abduljabbar da dan gwagwarmaya, Sowore. Hoto: Omoleye Sowore.
Source: Twitter

Halayen Abduljabbar da Sowore ya gano

'Dan gwagwarmayar ya bayyana malamin a matsayin mutum mai ilimi da tawali'u wanda ya nuna dogaronsa ga Allah duk da halin da yake ciki.

Sowore ya ce Abduljabbar ya fada musu cewa Allah yana kare shi kuma ya yi alkawarin ci gaba da jan hankalin al'umma har karshen rayuwarsa.

Ya kara da cewa:

"Duk da haka, mun tarar da mutum mai tawali’u, mai ilimi, wanda bai karaya ba, yana fuskantar jarabawa cikin nutsuwa da dogaro ga Allah.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Sowore ya fadi abin da ya sa ake tsare da malamin, ya sha alwashi

"Ya fada mana cewa Allah yana kare shi, kuma zai ci gaba da kare koyarwar Allah har karshen rayuwarsa duk da zaluntarsa da ake yi."

Sowore ya kuma zargi tasirin siyasa a cikin lamarin Malam Abduljabbar inda karara ya zargi Ganduje wanda ya rike mukamin gwamnan jihar a lokacin da hannu a lamarin.

Ya ce sun karɓi takardun daukaka kara, kuma za su nazarce su sosai, domin abin da ake nema shi ne adalci da kare addini daga masu amfani da shi.

Sowore ya tsoma baki kan lamarin Abduljabbar

A baya, kun ji cewa dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya koka kan cigaba da tsare fitaccen malamin addini a Kano bayan laifin batanci.

Ya bayyana cewa tun da dadewa ya yi niyyar kai wa malamin ziyara a kurkuku, amma hakan bai samu ba.

Sowore ya yi kira da a kawo ƙarshen duk wani nau’in danniyar addini a Najeriya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi a mutunta ‘yancin kowa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.