Tinubu zai Je Afrika ta Kudu Taron G20 yayin da Matsalar Tsaro Ta Kara Kamari

Tinubu zai Je Afrika ta Kudu Taron G20 yayin da Matsalar Tsaro Ta Kara Kamari

  • Fadar Shugaban Kasa ta ce halartar Shugaba Bola Tinubu taron G20 a Afirka na da muhimmanci ga makomar nahiyar
  • An ce Tinubu zai tattauna batutuwan tsaro, tattalin arziki da sababbin damammakin kasuwanci ga Najeriya a yayin taron
  • Hakan na zuwa ne yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, zai je Kebbi bayan sace dalibai mata a makaranta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cikakken dalilin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tashi zuwa Afirka ta Kudu da Angola domin halartar taron G20.

Ta yi bayanin ne kasancewar shugaban zai yi tafiya duk da cewa matsalolin tsaro na ƙara ta’azzara a Najeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya
Shugaban Najeriya yayin da zai yi wata tafiya a baya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A cewar sanarwar da Dada Olusegun ya fitar a X, tafiyar ba yawon duniya ba ce, illa wani muhimmin mataki ga martabar Najeriya da kuma tsare-tsaren haɗin gwiwa na Afirka.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi halin kunci da ta shiga bayan sace dalibai mata a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan Tinubu taro Afrika ta Kudu

A cikin bayanin Dada Olusegun, an ce kasancewar taron G20 karon farko a nahiyar Afirka alama ce mai muhimmanci ga ci gaban nahiyar, kuma dole Najeriya ta kasance a matsayin jagora.

Fadar shugaban kasa ta ce akwai muhimman batutuwa da Tinubu zai tattauna da shugabannin duniya domin inganta matsayin Najeriya a siyasance da tattalin arziki.

“Halartar shugaba Tinubu za ta nuna matsayin Najeriya wajen yabawa wannan sabon tarihi, da kuma amfani da damar wajen tabbatar da rawar da Afirka za ta taka a harkokin duniya.”

A cewar bayanin, Tinubu zai yi amfani da taron wajen ci gaba da tattaunawar da ya yi a taron G20 da ya gabata a Rio, inda zai gana da shugabanni daban-daban na duniya.

Hada kai da duniya wajen inganta tattali

Bayanan sun nuna cewa taron zai ba da damar gano sababbin damammakin zuba jari, da kuma ƙarfafa dangantaka da manyan ‘yan kasuwa da shugabannin tattalin arziki na duniya.

Kara karanta wannan

Tinubu zai nada jakadu bayan DSS ta mika sunayen mutanen da ta tantance

An bayyana cewa wannan wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin Tinubu na jan hankalin masu saka jari zuwa Najeriya.

Tinubu zai yi magana kan tsaro

An ce saboda tsaro zai kasance cikin abubuwan da za a tattauna, Tinubu zai yi amfani da taron wajen bayyana wa duniya ainihin yanayin da Najeriya ke ciki.

Fadar shugaban kasa ta ce:

“Taron zai ba da dama ga shugaba Tinubu wajen samar da sababbin yarjejeniyoyi da haɗin gwiwa tare da ƙasashe da ƙungiyoyin duniya domin yaki da ta’addanci a Najeriya da Afrika.”

Ayyukan gwamnati za su cigaba a Najeriya

Domin tabbatar da cewa babu gibi a harkokin gwamnati yayin da shugaba ke wajen ƙasa, an tura mataimakin shugaban kasa zuwa Kebbi.

Shettima zai je jihar Kebbi ne bayan sace dalibai mata 25 da aka yi a makarantar GGSS Maga a ranar Litinin.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a ofis. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

An ce Shettima zai jagoranci haɗin gwiwar hukumomin tsaro da na agaji domin duba yadda za a ceto matan da aka sace.

Amurka za ta fara bincike kan Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun fitar da matsaya kan daliban Kebbi da aka sace

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar Amurka za ta fara gudanar da bincike game da zargin kisan kiyashi da aka ce ana yi wa Kiristoci a Najeriya.

Bayanin da aka samu game da binciken ya nuna cewa an gayyaci wasu mutane daga Najeriya domin tattaunawa.

Za a fara binciken ne duk da cewa gwamnatin Najeriya ta karyata cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng