Yan Bindiga Sun Dawo, Sun Hana Manoma Taba Amfanin Gona sai da Harajin Miliyoyi

Yan Bindiga Sun Dawo, Sun Hana Manoma Taba Amfanin Gona sai da Harajin Miliyoyi

  • Yayin da ake kokarin kwashe amfanin gona a yankunan karkara da dama a Najeriya, yan bindiga sun sake dawowa domin karbar kudi
  • An tabbatar da cewa mutanen ƙauyuka a karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sun ce ’yan bindiga suna tilasta musu biyan kuɗin “girbi”
  • Maharan sun ce dole ne sai sun biya makudan kudi na miliyoyi kafin su shiga gonakinsu, duk da wahalar da ake ciki na rashin kudi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tsafe, Zamfara - Mutanen ƙauyuka a ƙaramar hukumar Tsafe ta Zamfara sun bayyana halin da suke ciki game da matsin yan bindiga a yankunansu.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindiga yanzu suna karɓar kuɗin “shiga gona” kafin manoma su taba amfaninsu wanda ya jefa su cikin tashin hankali.

Yan bindiga sun sanya haraji ga manoma a Zamfara
Karamin ministan tsaro wanda ya fito daga Zamfara, Bello Matawalle. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni kan matsalolin tsaro ya wallafa a manhajar X da aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ajalin ƙanin kwamishina ana tsaka da zaman makoki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun saba kakaba wa manoma 'haraji'

Wannan ba shi ne karon farko ba da manoma ke shiga mummunan yanayi musamman a wannan lokaci na girbin amfanin gona.

Tsawon shekaru da aka fara samun matsalar tsaro a yankunan Arewa maso Yamma, yan bindiga na sanya haraji kafin fara girbe amfani.

Wannan danyen aiki yana kara jefa al'umma cikin matsala saboda rashin kudin da za su biya da asarar da za su yi bayan sayar da amfanin gonan.

Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, daya daga cikin jihohi da yan bindiga suka addaba. Hoto: Legit.
Source: Original

Yawan miliyoyi da ake bukata daga manoma

Majiyoyi sun bayyana cewa ana tilasta wa wasu al’ummomi biyan tsakanin miliyan biyar zuwa miliyan 20, domin kawai su samu damar shiga gonakinsu ba tare da tsangwama ba.

Bayanan mazauna sun nuna cewa matsalar ba ta tsaya nan ba, saboda ko bayan an biya, ’yan bindigan kan sake sakin shanunsu su lalata abin da mutane suka noma.

Wasu manoma sun ce ba za su iya yin korafi ba saboda tsoron a kashe su, domin ƙaramar magana za ta iya zama dalilin rasa rai a yankin.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Korafin al'umma game da zaluncin 'yan bindigan

Al’umma suna cewa an yashe su gaba ɗaya, suna tambayar yadda wannan zalunci ke ci gaba ba tare da neman mafita ba, da kuma mamamakin abin da shugabanni ke yi wajen kare rayukansu.

Ga mazaunan Tsafe, abin da ke faruwa ba kawai rashin tsaro ba ne, illa rashin kariya ga manoma da gaza kare al’umma da suka dogara da noma.

Jama'a da dama na sake kira kan yadda za su samu kariya game da wannan zalunci duba da cewa amfanin gona ba zai iya biya musu wadannan kudade ba.

'Yan bindiga sun kakaba haraji a Sokoto

A wani labarin, al’ummar Bazar a Yabo ta jihar Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar ta taimaka musu wajen biyan harajin da ‘yan bindiga suka kakaba musu.

Mutanen yankin sun bayyana cewa rashin biyan harajin na iya janyo kai musu hari da kuma lalata amfanin gonarsu da ya kammala nuna.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Dauda Umar, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki da sace mutane bakwai tare da sace kayayyaki masu daraja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.