An Sake Rashin Babban Dan Kasuwa a Kano, Abba Kabir Ya Tura Sakon Ta’aziyya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sakon ta'aziyya game da rasuwar fitaccen dan kasuwa a jihar Kano da ya yi fama da jinya
- Mai girma Abba Kabir ya nuna alhini kan rasuwar Alhaji Ado Lamco, babban ɗan kasuwa a fannin kayan magunguna
- Ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon Kano mai jajircewa wajen tallafa wa jama’a, yana yaba gudummawarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga jimami a jihar Kano bayan sanar da rasuwar babban dan kasuwa a bangaren magunguna wanda ya ba da gudunmawa sosai.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna alhininsa kan rasuwar Alhaji Ado Aminu Mai Shinkafa bayan ya sha fama da jinya.

Source: Facebook
An yi rashin 'dan kasuwa a jihar Kano
Legit Hausa ta samu wannan sanarwa ce daga shafin Facebook na sakataren yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature D/Tofa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa marigayin dan kasuwar shi ya kafa shaharrarren kamfanin 'Lamco Pharmacy' a jihar Kano.
Alhaji Ado Lamco ya rasu a asibitin Cairo ranar Litinin 17 ga Nuwamba 2025 bayan dadewa yana jinya, inda ya rasu yana da shekaru 70.
Sanarwar ta ce marigayin ya kasance gwarzon mutum, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimaka wa al’umma da bunkasa masana’antar magunguna.
Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da abokansa da al’ummar kasuwanci, yana rokon Allah ya jikansa ya ba shi Aljannah Firdausi.
Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa gawarsa za ta iso Najeriya daga ƙasar Masar ranar Alhamis 20 ga watan Nuwambar 2025, domin gudanar da jana’iza bisa tsarin Musulunci.

Source: Facebook
Yabon da marigayin ya samu daga jama'a
Mutane da dama sun nuna bakin ciki kan rashin mutumin da suke bayyanawa a matsayin dattijon kirki mai haba-haba da jama'a.
Wani Yahaya Mohd Usman ya tuna irin zaman da suka yi da marigayin lokacin da ya kama haya a shagunan marigayin da ya gina.
Yahaya ya wallafa a Facebook inda ya ke jimamin rasuwar dattijon tare da yi masa addu'ar Ubangiji ya jikansa ya kuma gafarta masa zunubansa.
Ya ce:
"A shekarar 2002 lokacin da nake dab da bude ofishina na waya na biyu a Kano, a kusa da ƙofar AKTH, a lokacin ne Alhaji Ado ya gama gina wasu shaguna a wurin.
"Na karbi hayar ɗaya daga cikinsu, shi kuma ya bude sabon reshen Lamco Pharmacy a cikin ɗaya daga cikin shagunan. mun yi mu’amala kamar ’yan uwa tsawon shekaru da dama.
“Alhaji Lamco” kamar yadda muke kiransa, mutum ne mai ƙwazo, mai nutsuwa, mai halin kirki, kuma babban ɗan kasuwa da ya yi nasara."
Durbin Kano: Abba ya yi jimamin rasuwar basarake
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar Durbin Kano, Muhammad Lawan Koguna.
Abba ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da jama'ar jihar Kano bisa wannan rashi, inda ya yi addu'ar Allah ya gafarata masa.
Gwamnan ya ce rasuwar Durbin Kano babban rashi ne ga kasa baki daya, wanda ya bar gibin da zai wahala a iya cikewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

