An Yi Kutse cikin Wayoyin Hannun Fitattun Attajirai Dangote da Otedola

An Yi Kutse cikin Wayoyin Hannun Fitattun Attajirai Dangote da Otedola

  • Wasu masu kutse sun shiga wayoyin hannun fitattun attajirai a Afrika, Alhaji Aliko Dangote da Femi Otedola a cikin mako guda
  • Rahotanni sun bayyana cewa bayan masu kutsen sun yi nasarar shiga wayoyin, sun nemi a basu kudi da sunan attajiran
  • Fitattun 'yan kasuwan biyu, kuma aminan juna da suka dade suna abokantaka sun fuskanci matsalar a lokuta mabanbanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Wasu maharan yanar gizo sun kutsa cikin wayoyin hannu na Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote.

Rahotanni sun bayyana cewa sannan sun yi nasarar kutsawa cikin wayar hannun abokinsa, Femi Otedola, shugaban First HoldCo Plc.

An yi wa wayoyin hannun Dangote da Otedola kutse
Alhaji Aliko Dangote tare da Femi Otedola Hoto: Adekalu Michael
Source: Facebook

Majiyoyi daga bangarorin mutanen biyu sun tabbatar wa jaridar The Cable cewa an kwace cikakken ikon amfani da wayoyin su cikin makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ajalin ƙanin kwamishina ana tsaka da zaman makoki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi Dangote da Otedela kutse

Rahotanni sun tabbatar da cewa kutsen da aka yi wa manyan 'yan kasuwan biyu ya tayar da hankulan ma'aikatan su.

Rahotanni sun nuna cewa an yi wa Otedola kutse sau ɗaya, sai dai lamarin ya fi tsanani ga Dangote domin an yi masa kutse har sau biyu cikin kwanaki biyu.

Wannan ya haifar da tambayoyi masu yawa kan yadda maharan suka yi nasarar tsallake matakan tsaro a wayoyin masu faɗa a ji irin su.

Hankulan ma'aikatan Dangote da Otedola sun tashi
Femi Otedola, Alhaji Aliko Dangote Hoto: FemI Otedola/Dangote Industries
Source: Facebook

Har yanzu ba a tabbatar ba ko sun samu mayar da cikakken ikon wayoyinsu, amma majiyar da ta yi magana ta shaida cewa maharan sun riga sun fara neman kuɗi daga Dangote da Otedola.

Majiyar ta ce:

“Masu kutse suna neman kuɗi daga mutanen biyu."

Yadda aka shiga rudani kan Dangote da Otedola

Rahoton ya ci gaba da cewa lamarin da ya faru da abokan biyu bai yi wa jami'ansu dadi ba, duk da har yanzu babu cikakken bayani kan halin da da ake ciki.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Dangote da Otedola sun shafe shekaru suna abokantaka da junansu, har suna kiran juna ’yan’uwa a wurare daban-daban .

A baya-bayan nan Otedola ya halarci taron da Dangote ya bayyana shirin fadada masana’antar man fetur dinsa daga 650,000 zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.

A wurin taron ne Otedola ya sake bayyana Dangote a matsayin gwarzon Afrika, wanda ya kamata a rika alfahari da shi da duk nahiyar.

Matatar Dangote ta magantu kan farashin fetur

A baya, mun wallafa cewa matatar Dangote ta karyata cewa ta rage farashin man fetur a tashoshin mai saboda Shugaban Bola Tinubu ya janye harajin shigo da fetur da dizal.

A baya, matatar Dangote da ke Legas ta rage farashin man kowace lita daga wurin dakonsa daga N877 zuwa N828, lamarin da dwasu ke ganin saboda janye dokar Tinubu aka yi shi.

Matatar ta yi tir da shigo da man fetur mai mara inganci daga ƙasashen waje, domin a cewarta, irin wannan man mara kyau yana kawo cikas ga masana’antar cikin gida.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng