Kisan Kiristoci: CAN Ta Kira Trump kan Taimakon Najeriya, Yaki da Ta’addanci

Kisan Kiristoci: CAN Ta Kira Trump kan Taimakon Najeriya, Yaki da Ta’addanci

  • Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya kuma magana kan zargin kisan Kiristoci da ake yi a ƙasar
  • Okoh ya ce suna maraba da shawarar Amurka na taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar
  • Kungiyar ta jaddada cewa akwai “kisan ƙare-dangi na Kiristoci” a Najeriya, tana mai cewa CAN ba za ta gajiya ba wajen neman adalci da kariya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa tabbas ana kisan kiyashi kan mambobinta a kasar bayan zargin da Amurka ta yi.

Kungiyar ta ce abin maraba ne matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na yunkurin taimakawa Najeriya wajen yaƙi da kashe-kashe da kuma rashin tsaro a ƙasar.

CAN ta yi maraba da barazanar Trump
Shugaba Donald Trump da shugaban CAN, Daniel Okoh. Hoto: Donald J Trump, Christian Association of Nigeria.
Source: Facebook

Matsayar CAN kan barazanar Trump a Najeriya

Kara karanta wannan

Amurka za ta fara cikakken bincike kan Najeriya game da zargin kisan Kiristoci

Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar yayin buɗe taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na huɗu da aka gudanar a Jos, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin takaici ne ganin Najeriya na shiga manyan jaridun duniya saboda mummunan yanayi.

Amma idan hakan zai sa gwamnati ta ɗauki mataki wajen kare rayuka da samar da zaman lafiya, to al’ummar Kiristoci a ƙasar suna maraba da wannan kulawa.

A cewarsa:

“CAN ta yi magana a fili, kuma har yanzu mun tsaya a kan matsayarmu cewa ana kisan ƙare-dangi ga Kiristoci a Najeriya.”

Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, al’ummar Kirista na nan da karfinsu, domin haɗin kai da juriya.

Kiran da CAN ta yi ga shugabannin Kiristoci

Rabaran ɗin ya yi kira ga shugabannin Kirista da su ci gaba da jajircewa, addu’a da ƙarfafa zukata, tare da cigaba da yada saƙon bege a cikin yanayin bakin ciki da damuwa.

Ya tabbatar da cewa CAN ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman adalci ga mambobinta da kuma kira da a ɗauki matakan kariya.

Kara karanta wannan

Fafaroma Leo ya sanya Najeriya a cikin kasashen da ake tsananta wa kiristoci

“Mu a CAN ba za mu daina ba. Za mu ci gaba da neman adalci. Za mu ci gaba da kira ga halin da ake ciki."

- Daniel Okoh

Kungiyar CAN ta tabbatar ana kisan Kiristoci
Shugaban kungiyar CAN, Daniel Okoh. Hoto: Shugaba Donald Trump da shugaban CAN, Daniel Okoh. Hoto: Christian Association of Nigeria.
Source: Facebook

Shawarar CAN game da yan gudun hijira

Haka kuma ya yi kira da a mayar da dukkan ’yan gudun hijira (IDPs) zuwa asalin yankunansu, yana mai cewa matsalolin da suka dade suna fama da su sun zama abin kunya ga ƙasa.

Shugaban CAN ya ce zaɓen birnin Jos a matsayin wurin taron ya kasance mai ma’ana sosai, domin birnin ya sha wahala, an yi kuka, ya yi addu’a kuma har yanzu yana da cikin inda ake ban gaskiya.

Ya ce yana fatan sakamakon taron zai ƙarfafa haɗin kan iklisiya da kawo zaman lafiya ga ’yan Najeriya gaba ɗaya, cewar Daily Post.

Barazanar Trump: Shugaban CAN ya yi karin haske

Kun ji cewa shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na Arewa, Fasto Joseph Hayab, ya yi tsokaci kan kalaman Donald Trump.

Fasto Hayab ya bayyana cewa an yi kalaman shugaban kasar Amurka gurguwar fahimta kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yar majalisa ta dura kan tsohon shugaban Amurka da ya saukakawa Najeriya kan addini

Shugaban na CAN ya bayyana cewa ya kamata a amince cewa ana kai wa Kiristoci hare-hare a wurare da dama a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.