Gwamnan Katsina, Dikko Radda Ya Dauki Mataki kan Malam Yahaya Masussuka
- Gwamnatin jihar Katsina ta samu koke cewa karatuttukan Malam Yahaya Masussuka na saba da ka’idojin shari’ar Musulunci
- Wannan koke ya sa sarkin Katsina ya shiga tsakani, amma a karshe aka ce babu wani ci gaba da aka samu daga bangarorin
- Bisa wannan, Gwamna Dikko Radda ya umarci Malam Yahaya da ya bayyana gaban kwamitin malamai domin kare kansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnatin Katsina ta umurci sanannen malamin addini, Malam Yahaya Masussuka, da ya gurfana gaban kwamitin malaman addini na jihar.
Gwamnatin ta umarci Masussuka ya je gaban komitin ne domin kare kansa kan zargin cewa karantarwar da yake yi tana sabawa tsarin koyarwar Musulunci.

Source: Facebook
Wannan umarni ya biyo bayan jerin koke-koke da gwamnati ta karɓa, ciki har da zargin cewa wasu daga cikin karatuttukansa sun sabawa ka’idodin Shari’a, in ji rahoton KTTV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda kuma, Malam Yahaya ya kai kara cewa mambobin kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a, watau Izala, na barazanar kai masa hari saboda karatuttukansa.
Sarkin Katsina ya gayyaci Malam Masussuka
Don magance matsalar tun daga tushe, gwamnatin jihar ta mika batun zuwa Fadar Masarautar Katsina ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman (CFR).
Sarkin ya gayyaci Malam Yahaya da sauran malaman domin tattaunawa a fadar sa, inda ya gargadi kowane malami da kada ya yi wa’azi ko koyarwa da zai bata wa sauran Musulmi rai ko tayar da rigima.
Sai dai duk da wannan shiga tsakani, rahotanni sun nuna cewa rikicin bai lafa ba, lamarin da ya sa gwamnati ta dauki mataki na gaba.
Gwamna Radda ya ba da umurnin yin bincike
A cewar sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya fitar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya ba da umarni cewa Malam Yahaya ya zo ya kare kansa gaban kwamitin malamai.
Kwamitin zai binciki zarge-zargen, sannan a fitar da tsare-tsare da ka’idojin wa’azi da koyarwa a fadin jihar.
Gwamnati ta yi gargadi cewa duk wanda ya karya wadannan ka’idoji da za a kafa nan gaba, za a dauki mataki mai tsauri a kansa.
Martanin 'yan Najeriya kan gayyatar Masussuka
Legit Hausa ta tattaro kadan daga ra'ayoyin jama'a game da gayyatar da aka yi wa Malam Yahaya Masussuka:
Buhari Haruna:
"Alhamdulillah Allah ya kara taimakon Sunnar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam"
Haruna Abu Yazid:
"Ba mu tsoron yin mukabala muddin za ayi ta akan gaskiya da adalci."
Yusuf Sadeeq Wunti:
"Gwamna Katsina zai kashe kansa a siyasa."

Source: Facebook
Isma'il Abubakar:
"Wannan ba wani abu bane illa salon kauda hankalin mutane daga rashin tsaron da jihar ke ciki a fada ma rigimar addini da ba zata haifar da ɗa mai ido ba."
Jaafar Sani:
"Ƙarya ta ƙare. Su masussuka za a sha mutsutstsuka."
Mahamud Yahuza:
"Babu yanda za’ayi Izala su samu sa’ar Masussuka wallahi domin shi dai Alkur’ani ya yarda da shi, bai yadda da sauran littattafai ba."

Kara karanta wannan
PDP ta rikice: Gwamnoni 2 sun nesanta kansu daga korar Wike, Fayose daga jam'iyya
Jabir At-tidjaniy:
"Wannan shi ne mafi girman kuskuren da gwamnati za ta yi. Kuma insha Allah, ya kashe siyasar sa indai ya biyewa wannan 'yan Izalar"
Jalo Jalingo na son yin mukabala da Masussuka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya bukaci gwamnan Katsina ya shirya muƙabala tsakanin malamai da Yahaya Masussuka.
Fitaccen malamin addinin ya ce wannan mataki ya fi dacewa fiye da muƙabalar da aka shirya a Kano tsakanin malamai da Abduljabbar Kabara.
A yanzu haka dai idanu sun karkata kan gwamnatin Katsina ko za ta amsa wannan kira domin shirya mukabalar tsakanin Masussuka da malaman Izala.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

