Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Ƙanin Kwamishina Ana tsaka da Zaman Makoki
- Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai farmaki ana tsaka da zaman makoki inda suka hallaka wani daga cikin masu jimami
- An shelanta mutuwar Christopher Igwe, dan'uwan kwamishina a gwamnatin Ebonyi bayan wasu ’yan fashi sun bude wuta
- Shaidu sun ce wannan lamari ya faru ne lokacin da mamacin da ’yan uwansa ke shirin tafiya addu'a na musamman
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Ebonyi - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun harbe wani daga cikin yan uwan Kwamishina yayin zaman makoki.
An tabbatar da cewa maharan sun bindige Christopher Igwe da aka fi sani da Bombay, wanda bai san hawa ba bare sauka.

Source: Original
Rahoton Leadership ya ce marigayin kanin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu ne na jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan
Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga suka kashe kanin Kwamishina
Kwamishinan ya tabbatar da cewa kisan ya jefa iyalinsu cikin alhini, kasancewar lamarin ya faru ne a garinsu Idembia Ishieke a karamar hukumar Ebonyi.
Shaidu sun bayyana cewa mamacin da ’yan uwansa suna shirin halartar addu’ar tunawa da wani danginsu lokacin da ’yan fashi suka iso wurin ne.
Rahoto ya nuna cewa dillalin iskar gas da aka sako yana cikin korafi, hakan ya sa ’yan fashin suka bude wuta yayin kokarin tserewarsu.
Wata majiya ta ce:
"Wani dillalin iskar gas ya ruga zuwa wurinsu domin ya shaida cewa ’yan fashi sun sace shi kuma sun gudu a kan babura guda biyu.
Jim kaɗan bayan haka, ’yan fashin, wadanda suka yi kama da wadanda suka rasa hanyar tserewa, suka dawo.
"Wanda abin ya faru da shi ya yi ihu domin ya sanar da mutane, da suka lura da hakan, ’yan fashin suka fara harbi ko ina yayin da suke kokarin tserewa."

Source: Twitter
An tabbatar da mutuwar kanin kwamishina
Daga bisani an garzaya da wadanda abin ya rutsa da su domin ceto lafiyarsu amma aka yi rashin sa'a kanin kwamishinan ya rasu.
An kai Christopher da dillalin gas asibitin Alex Ekwueme Abakaliki, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar Christopher yayin da dayan ke karbar magani.
"An garzaya da mamacin da dillalin gas, wanda suma suka samu raunukan harbi a wurare masu muhimmanci na jikinsu, zuwa Asibitin Koyarwa na Alex Ekwueme, Abakaliki.
"A can ne likitoci suka tabbatar da mutuwar kanin kwamishina, yayin da ake cewa dayan wanda ya tsira har yanzu yana jinya saboda raunukan harbin da ya samu."
- Cewar majiyar
’Yan sanda sun ce sun isa wurin bayan samun rahoton amma ’yan fashin sun tsere, kuma an fara bincike don gano wadanda suka yi kisan.
Zamfara: 'Yan bindiga sun harbe jigon APC
An ji cewa rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da ta'azzara yayin da aka kashe babban dan siyasa.

Kara karanta wannan
Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a kan hanyar Tsafe, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.
An bayyana marigayin wanda jigon APC ne a matsayin jajirtaccen mutum mai kishin yankin da cewa rasuwarsa babban gibi ce ga jama’ar Shinkafi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
