Atiku Ya Ba Tinubu Satar Amsa kan Hanyar Magance Rashin Tsaro
- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi alhini kan kisan da 'yan ta'addan ISWAP suka yi wa babban jami'in soja
- Atiku Abubakar ya bayyana kisan Birgediya Janar M. Uba a matsayin alamar da ke nuna farfadowar 'yan ta'adda
- Hazakalika, ya bayyana matakin da zai dauka domin kawo karshen 'yan ta'adda da a ce shi ne shugaban kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matuƙar takaici da bakin cikinsa kan kisan Birgediya Janar M. Uba.
'Yan ta'addan ISWAP ne suka hallaka Birgediya Janar M. Uba bayan sun yi wa dakarun sojoji kwanton bauna.

Source: Facebook
Atiku Abubakar ya yi martani kan kisan babban jami'in sojan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, a ranar Talata, 18 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ISWAP sun kashe babban soja
Rahotanni sun ce an kashe Birgediya Janar Uba ne lokacin da 'yan ta'addan suka yi wa dakarun sojoji da jami’an ‘Civilian Joint Task Force' (CJTF) kwanton ɓauna a hanyar Damboa, kusa da Wajiroko, jihar Borno.
'Yan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne a ranar Juma’a yayin da suke jigilar makaman yaki.
Me Atiku Abubakar ya ce kan lamarin?
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin gazawar shugabanci, yana kuma zargin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da maida hankali kan danniya ga ‘yan adawa maimakon gudanar da aikinsa na babban kwamandan rundunonin sojojin Najeriya.
Atiku ya kuma soki yadda rundunar sojoji ta gaza bayar da sahihin bayani cikin gaggawa game da abin da ya faru.
“Mutuwar Birgediya Janar Musa, tare da sojojin da suka rasu da ke karkashinsa, mutuwa ce wadda ke nuna sake farfadowar ‘yan ta’adda, abin da Najeriya ba za ta iya ɗauka ba."
- Atiku Abubakar
Wace shawara Atiku ya ba Tinubu?
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, da shi ne shugaban kasa, zai umurci sojoji su mamaye jihar Borno ko duk wata jiha da rikici ya yi katutu, har sai sun share dukkan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Source: Facebook
“Ga shugaban kasa, tsaron rayukan ‘yan kasa shine babban aikin ka. Dole ka yi aikinka ko ka amince da rashin kwarewa sannan ka nemi taimako ko ka yi murabus.”
- Atiku Abubakar
Atiku ya jaddada cewa dole a nuna kulawa da mutunta sojojin da ke sadaukar da rayukansu domin kare kasa, yana mai cewa Najeriya ta kasa sauke hakkinsu yadda ya kamata.
Ya kammala da kira ga ‘yan Najeriya da jami’an tsaro su kara jajircewa yana mai cewa wannan mawuyacin lokacin zai wuce.
Atiku ya yi Allah wadai kan sace dalibai
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alhini kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin sabon tabbaci na lalacewar tsaron Najeriya, yayin da yake Allah wadai da sace daliban da 'yan bindigan suka yi.
Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake fasalin tsaron kasa cikin gaggawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


