Katsina: Wasu Mutum 4 Sun Bayyana yadda Suke Mika Bayanan Sirri ga 'Yan Ta'adda

Katsina: Wasu Mutum 4 Sun Bayyana yadda Suke Mika Bayanan Sirri ga 'Yan Ta'adda

  • Jami’an hukumar tsaron Katsina sun kama wasu da ake zargin ’yan leƙen asiri ne ga ’yan bindiga a Kankia domin kai hari wasu sassan jihar
  • Wadanda aka kama sun amsa cewa suna tura bayanan sirri ga kungiyoyin ’yan ta’adda da ke kai hare-hare zuwa garuruwa da dama a yankin
  • Yanzu haka ana ci gaba da bincike, yayin da bidiyon tambayoyin da ake musu ya fara yawo kuma dukkaninsu sun amsa laifin da ake zargin sun aikata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Jami’an hukumar tsaron jihar Katsina sun cafke wasu mutane guda hudu da ake zargi da bai wa ’yan bindiga bayanan asiri a ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen ne bayan dogon bincike kan yadda ake samun harin ’yan ta’adda a yankin, kuma yanzu haka ana ci gaba da zurfafa bincike a kan lamarin.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

Masu taimaka wa yan ta'adda da bayanan sirri sun shiga hannu
Hoton gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda Hoto: Umar Dikko Radda
Source: Facebook

Wani mai sharhin tsaro a Arewa masi Yamma, Bakatsine ya wallafa bidiyoyin mutanen da aka kama a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katsina: An kama masu aiki da 'yan ta'adda

Wasu daga cikin wadanda aka kama sun amsa cewa suna taka rawar wajen taimaka wa ’yan ta’adda kai hare-hare a Kankia da makwabtansu.

Ɗaya daga cikin wadanda aka kama, mai suna Mani, ya bayyana cewa yana aiki tare da wasu abokan aikinsa, ciki har da Murtala, Haru Galadima, Maikudi Ahmadu da Dan Binta.

Ya ce lallai yana mika bayanan da ke taimaka wa ’yan ta’adda gano inda jami’an tsaro ke tsaye ko yadda za su shigo gari ba tare da tangarda ba.

Wadanda aka kama sun amsa laifinsu
Taswirar jihar Katsina, inda aka kama masu aiki da 'yan ta'adda Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mani ya kara da cewa bayanansu ne suka taimaka wajen sace wata Hajiya da ɗanta Babangida a Kidangi, a Kankia.

Haka zalika, Bala Iliyasu Galadima, wani da ya shiga hannun jami’an tsaro, ya tabbatar cewa yana aika bayanai ga ’yan bindiga ta wayar hannu.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka afka wa mazauna Zamfara, sun kwashe sama da mutum 60

Ya ce yana sanar da su ko akwai motsin jami’an tsaro ko babu, wanda hakan ke ba wa ’yan ta’addan damar kai farmaki cikin kwanciyar hankali.

Ana binciken masu aiki da 'yan ta'adda

Murtala daga Tashar Lado, wani matashi dan shekara 35, ya tabbatar da cewa ya sha mika bayanai ga ’yan bindiga.

Ya ce yana aiki da wani Shafi’u na Cindawa da kuma KB na Zamfarawa, tare da Tukur Dan Binta, wadanda ake zargin suna mika bayanai ga 'yan ta'adda.

A nasa bangaren, Dahiru daga Kusada ya amsa cewa shi ma yana taimaka wa ’yan ta’adda ta hanyar nuna musu gidajen da za su shiga.

Ya ce yana sanar da su gidajen da suka fi dacewa a kai hari, musamman a yankin Kulle Gidi, kuma 'yan ta'addan sun samu nasara a lokacin.

Katsina: 'Yan ta'adda sun kashe bayin Allah

A baya, mun wallafa cewa a wani mummunan hari da aka kai a Doguwar Ɗorawa, kusa da Guga a ƙaramar hukumar Bakori, jihar Katsina, ‘yan bindiga sun kashe shugabannin al’umma biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da daddare a inda aka kashe Alhaji Bishir da ɗan uwansa, Alhaji Surajo, wadanda suke cikin manyan dattawan kauyen da yankin baki daya.

Kara karanta wannan

Mansur Sokoto ya fadi yadda 'yan bindiga suka kashe shugaban MSSN a Kebbi

Wani jigo a garin Guga, Mahadi Danbinta Guga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun shafe tsawon awa ɗaya suna aikata mugun aikin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng