Hadimin Buhari Ya Karyata 'Dan Majalisar Amurka kan Sace Daliban Kebbi a 'Yankin Kiristoci'
- Dan majalisar Amurka, Riley Moore ya yi Allah-wadai da sace ɗalibai 25 na Makarantar GGCSS Maga tare da kiran yin addu’a
- Bashir Ahmad ya musanta ikirarin Moore cewa harin ya faru ne a “yankin Kirista,” yana cewa maganar sam ba haka ba ne
- Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana aiki tukuru domin ceto daliban da aka sace ranar Litinin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dan majalisar tarayya daga Amurka, Riley Moore, ya bayyana damuwarsa kan harin da ’yan bindiga suka kai GGCSS Maga, a yankin Danko-Wasagu na jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe mataimakin shugaban makarantar tare da sace ɗalibai 25.

Source: Getty Images
Moore ya yi rubutu a shafin X a ranar Talata, inda ya ce abin da ya faru ya girgiza shi, yana mai kira ga jama’a su taya shi yin addu’a domin ceton ɗaliban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bayan rubutun nasa, wasu daga cikin ’yan Najeriya sun yi masa raddin cewa ya yi kuskure wajen bayyana yankin da aka kai harin.
Maganar 'dan majalisar kan daliban Kebbi
A cikin rubutun da Moore ya wallafa, ya yi zargin cewa lamarin ya faru ne a yankin da Kiristoci suka fi yawa a Arewacin Najeriya.
Ya ce:
“Don Allah ku taya ni yin addu’a domin ’yan mata 25 da aka sace da kuma roƙon rahama ga mataimakin shugaban makarantar da aka kashe.”
Ya ƙara da cewa:
“Ko da yake ba mu da cikakken bayani kan wannan mummunan hari, mun san an kai shi ne a yanki na Kirista a Arewacin Najeriya.”
Haka kuma, Moore ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su dauki mataki mai ƙarfi, yana mai cewa:
“Dole Gwamnatin Najeriya ta yi aiki don kawo ƙarshen wannan tashin hankali mai yawa.”
Bashir Ahmad ya ci gyaran dan majaliar Amurkan

Kara karanta wannan
Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi
Wannan ikirari na Moore ya haddasa martani daga tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad wanda ya yi masa gyaran kuskuren a fili.
Bashir Ahmad ya bayyana a X cewa:
“Tare da godiya ga damuwarka da addu’o’in da ka yi, yana da muhimmanci a gyara abu guda — harin ba a wani yanki na Kirista aka kai shi ba.”
Ya ƙara da cewa:
“An kai harin ne a cikin al’ummar Musulmi, kuma waɗanda abin ya shafa su ma Musulmai ne. Wannan shi ne dalilin da muke cewa ’yan Amurka ba ku fahimci rikice-rikicen tsaron Najeriya ba, ko kuma kuna sakin wasu labarai da ka iya lalata haɗin kanmu.”

Source: Facebook
Jawabin Bashir Ahmad ya sake tayar da muhawara kan yadda wasu ƙasashen waje ke bayyana rikicin tsaro a Najeriya, musamman batun da ake yawan dangantawa da “cin zarafin Kirista,”
Martanin Najeriya kan daliban Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa ba za ta yi shiru ba game da daliban da aka sace a Kebbi.
A wata sanarwa, gwamnatin ta ce tana yin aiki kafada-da-kafada da jami’an tsaro don tabbatar da cewa ɗaliban sun dawo gida lafiya.
A cewar gwamnati, ana daukar duk matakan da suka dace domin ganin an kawo ƙarshen kai wa makarantun Arewa maso Yamma hari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

