Dalilin da Ya Sa Sheikh Ahmad Gumi Ya Kafe kan Batun Tattaunawa da Yan Bindiga
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce da mutane sun san hadarin da yake shiga wajen zuwa tattaunawa da yan bindiga da sun yaba masa
- Malamin addinin Islaman ya dage cewa babu wata mafita da za ta kawo karshen ta'addanci a Arewa face zama a teburin tattaunawa
- Ahmad Gumi ya bayyana dalilin da ya sa duk da sukar da ake yi masa, ya kafe kan bakarsa ta sasanci da 'yan ta'adda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigera - Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na ci gaba da shan suka daga bangarori da dama kan matsayarsa ta sasanta qa da 'yan bindiga.
A karshen makon da ya gaba, wasu 'yan Najeriya suka fara kiraye-kiraye ga jami'an tsaro da su kama malamin domin a ganinsu, ya san wasu abubuwa game da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan
Sulhu da 'yan bindiga: Sheikh Gumi ya ragargaji masu sukarsa, ya fadi nasarorin da ya samu

Source: Facebook
Duk da wannan suka da yake sha, Sheikh Gumi ya fito a shafinsa na Facebook ya sake jaddada cewa yana nan kan bakarsa ta neman a sasanta da 'yan bindiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Gumi kan masu so a kama shi
Babban malamin ya kuma maida martani ga masu kiran a kama, yana mai cewa ba ya tsoron jami'an tsaro su damke shi a kokarinsa na ganin Arewa ta samu zaman lafiya.
Dr. Ahmad Gumi ya sha ba da shawara ga mahukuntan Najeriya kan yadda za a warware matsalar tsaro, a cewarsa zama teburin sulhu da yan bindiga ce kadai mafita.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce mutanen da ke kira a kama shi saboda kokarinsa na sasanta wa da ‘yan bindiga “jahilci” ne ya rufe su, irin jahilcin da ya ce ya rufe wasu daga cikin ‘yan bindiga da suke addabar yankin Arewa.

Kara karanta wannan
An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP
Wane hadari Sheikh Gumi ke shiga?
A wani sakon da ya wallafa, Gumi ya ce mutane ba su gane irin haɗarin da yake fuskanta ba duk lokacin da yake shiga daji domin sasanta rikici.
“Da sun san irin haɗarin da muke shiga don mu gana da waɗannan ‘yan bindiga, da maimakon su zage mu, yaba mana za su yi,” in ji shi.
Me yasa Gumi ke son sasanci da yan bindiga?
Ya ce dalilin da ya sa ya dage a sasanta da ‘yan bindiga shi ne yadda rikicin ke ci gaba da jefa Arewa cikin halin koma-baya, tare da hana jama’a noma da tilasta wa wasu barin garuruwansu.
“Mu ‘yan Arewa mu ne abin ya shafa, mu ake cutarwa. Idan muka zuba ido, ba mu yi wa al’umma da gwamnati adalci ba."

Kara karanta wannan
Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
"Muna ƙoƙarin nuna musu (yan bindiga) kuskurensu ne, mu ilmantar da su domin mun fahimci rashin ilimin addini ne ya raba su da hanya madaidaiciya.”
“Hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen ta’addanci ita ce a ba wa ‘yan bindiga ilimi, a karfafa musu imani tare da basu fata mai kyau.”
- Sheikh Ahmad Gumi.

Source: Facebook
Gumi ya gamsu da sulhu a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana gamsuwa da yadda mazauna Katsina ke sulhu da 'yan ta'adda.
Sheikh Gumi ya ce irin wannan matakin da aka dauka a Karamar Hukumar Sabuwa na sulhu da yan bindiga yana da matukar muhimmanci wajen dorewar zaman lafiya.
Malamin ya bukaci gwamnati da ta yi amfani da tsarin sake janyo hankalin masu dauke da makami kamar yadda aka yi da tsofaffin ’yan awaren Neja Delta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng