Gwamnan Kebbi Ya Daukarwa Iyayen Yaran da Aka Sace Alkawari

Gwamnan Kebbi Ya Daukarwa Iyayen Yaran da Aka Sace Alkawari

  • Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu dalibai mata na wata makarantar sakandire a jihar Kebbi
  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar da lamarin ya auku domin ganewa idonsa halin da ake ciki
  • Nasir Idris wanda ya gana da iyayen yaran da aka sace, ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin 'ya'yansu sun kubuta

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi magana kan sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi a wata makantar sakandiren jihar.

Gwamna Nasir Idris ya ce ya tabbatar wa iyayen daliban mata da aka yi garkuwa da su daga makarantar GGCSS, Maga, cewa ana yin dukkan kokari domin ceto ’ya’yansu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi

Gwamna Nasir Idris ya je ziyarar gani da ido garin Maga
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu Hoto: @NasirIdrisKIG
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 17 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bada tabbacin ne bayan ya kai ziyara Maga, inda lamarin ya faru kuma ya yi ganawar sirri da jami’an tsaro, shugabannin gargajiya da kuma iyayen daliban da aka sace.

'Yan bindiga sun sace dalibai a Kebbi

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 25 a daren ranar Lahadi daga makarantar da ke cikin karamar hukumar Danko/Wasagu.

A cewar majiyoyi, ’yan bindigan sun kashe Malam Hassan Makuku, wanda shi ne mataimakin shugaban makarantar, kafin su yi awon gaba da daliban mata.

Shaidu sun bayyana cewa 'yan bindigan sun dauki lokaci suna ta'asarsu ba tare da fuskantar wata turjiya, wanda hakan ya jefa mutanen garin cikin tashin hankali da alhini.

An ce Malam Hassan Makuku ya rasa ransa ne yayin da yake kokarin kare dalibansa a lokacin harin.

Kara karanta wannan

Shugaban sojoji ya dura Kebbi, ya ba dakaru umarni kan daliban da aka sace

Me Gwamna Nasir Idris ya ce?

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ya gana da iyayen yaran da 'yan bindigan suka sace, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

“Abin bakin ciki ya riga ya faru. Sun sace mana ’ya’ya. Mun zo nan, mun gani da idonmu, mun kuma gana da iyayen da aka sace wa ’ya’ya.”
“Mun ba su tabbaci, mun kuma ba su kwarin gwiwa tare da daukar musu alkawarin cewa za mu yi duk abin da ya kamata domin ganin an ceto ’ya’yansu.”

-Gwamna Nasir Idris

Gwamna Nasir Idris ya yi Allah wadai da sace dalibai mata
Gwamna Nasir Idris na jawabi a wajen wani taro Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamna Idris ya ce sun kuma bukaci iyayen da su kasance masu kwarin gwiwa, domin hukumomin tsaro za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ceto daliban.

Ya ce hakan shi ne dalilin zuwansu Maga don ganin halin da ake ciki da kuma karfafa gwiwar al’umma.

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mai girma Bola Tinubu, ta yi martani kan sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Sanata Anyanwu ya dora laifin abubuwan da ke faruwa kan gwamnoni 7

Gwamnatin ta bada tabbacin cewa ta umarci jami'an tsaro da su gaggauta kubutar da daliban da aka sace.

Hakazalika, ta bayyana cewa za ta dauki matakan yin rigakafi domin hana sake aukuwar irin hakan a nan gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng