Bayan Ficewar 'Yan Majalisa, Shugaban PDP a Taraba Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Taraba ta sake samun koma bayan murabus din shugabanta daga kan mukaminsa
- Alhaji Abubakar Bawa ya yi murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga jam'iyyar PDP ba tare da bata lokaci ba
- Shugaban na PDP ya bayyana cewa rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar na daga cikin dalilan sa suka sanya ya raba gari da ita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Taraba, Alhaji Abubakar Bawa, ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Hakazalika, shugaban na PDP ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar mai mulki a jihar Taraba.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa Alhaji Abubakar Bawa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin, 17 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa shugaban PDP ya fice daga jam'iyyar?
Alhaji Abubakar Bawa ya ce shawarar da ya yanke ta biyo bayan rikicin shugabanci da kuma shari’o’in da suka dabaibaye jam’iyyar PDP a matakin kasa.
“Ina so na sanar da ku da ma jama’ar Taraba cewa na yi murabus daga kasancewa mamba a jam’iyyar PDP, kuma na riga na rubuta wa shugaban gundumata takardar murabus.”
“Takardata na cewa: Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP tun daga 17 ga watan Nuwamba, 2025.”
- Alhaji Abubakar Bawa
Bawa ya bayyana cewa matakin nasa ya kasance ne bayan dogon tunani da nazarin rikice-rikicen da suka addabi jam’iyyar a matakin kasa, musamman rikicin shugabanci mai tsawo da shari’o’in da suka janyo rashin tabbas a tsarin PDP.
“Rikicin shugabanci da shari’o’in da suka daɗe suna faruwa sun haifar da rashin tsari, wanda ya sa ya zama da wuya na ci gaba da bin tafiyar jam’iyyar cikin wannan hali.”
- Alhaji Abubakar Bawa
Bawa ya hidimtawa PDP a Taraba
Jaridar Leadership ta ce ya bayyana cewa ya yi aikin jam’iyyar da gaskiya da amana tsawon shekaru, musamman a matsayinsa na shugaban PDP na jihar Taraba, yana mai gode wa jami’an jam’iyyar bisa amincewa da goyon baya da suka ba shi.

Source: Twitter
Bawa ya ce tafiyarsa a PDP ta kasance ta hidima, sadaukarwa da jajircewa ga dimokuradiyya, amma saboda kare mutuncinsa da ka’idojinsa, ya ga dacewa ya koma gefe domin tantance makomar siyasarsa.
A karshe, ya gode wa shugabannin jam'iyyar da mambobi bisa haɗin kai da zumunci da suka nuna masa a lokacin da yake jagoranci.
Shugaban majalisa ya fice daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.
Rt Hon. Kizito Bonzena, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan tare da sauran mambobi 15 na majalisar dokokin jihar.
Shugaban majalisar dokokin ta Taraba ya bayyana cewa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC ba don wata manufa ta kashin kansa ba, sai don maslahar jihar Taraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


