Gwamna Abba Ya Kara Gwangwaje Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da Mukami

Gwamna Abba Ya Kara Gwangwaje Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da Mukami

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Majalisar sarakunan Kano karkashin jagorancin Mai martaba Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II
  • Abba, wanda ya jagoranci kaddamar da majalisar, ya ce wannan mataki zai ba sarakuna damar taka rawa wajen kawo ci gaban al'umma
  • Muhammadu Sanusi II ya jinjinawa Gwamna Abba bisa ayyukan ci gaban da yake aiwatarwa domin inganta rayuwar mutanen Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dawo da Majalisar Sarakunan jihar domin inganta ayyukan sarakunan gargajiya.

Gwamnan ya kuma tabbatar da Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.

Gwamna Abba da Muhammadu Sanusi II.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafin Facebook yau Litinin.

Kara karanta wannan

Akpabio: Shugaban majalisar dattawa ya fadi halin da yake shiga kan kashe kashe a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II zai jagoranci sarakunan Kano

Sanarwar ta bayyana sauran sarakuna uku, na Gaya, Karaye da Rano a matsayin mambobin majalisar.

A yayin taron da aka gudanar a fadar gwamnati, Gwamna Abba ya bayyana cewa an farfado da majalisar da nufin samar da ingantaccen tsarin aiki ga masarautu domin su taka rawa wajen kare zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Kano.

Gwamnan ya jaddada cewa masarautu su ne tushen tarihi, masu raya al’adu, tsare dabi’u da hadin kai, kuma abokan tafiyar gwamnati wajen ciyar da al’umma gaba.

"Farfado da Majalisar Sarakuna a yau na kara nuna kudirin gwamnatarmu na tsare martabar al’adu da tarihin Kano, karfafa tsarin mulki, tare da zurfafa hadin kai tsakanin gwamnati da masarauta,” in ji Abba.

Abba ya dawo da martabar sarakuna

Gwamnan ya ce an kafa majalisar ne domin samar da wuri guda da sarakuna za su rika tattaunawa, yin shawarwari, da jagorantan al’amuran da suka shafi cigaban al’ummar Kano.

Kara karanta wannan

Bayan kashe kashen mutane, Tinubu ya tura jakadiyar wanzar da zaman lafiya Filato

Tun da farko, Mai ba gwamna shawara kan harkokin masarauta, Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, ya gabatar da tsokaci mai fadi kan tarihin masarautar Kano da alakar ta da masarautun Rano, Gaya da Karaye.

Farfesa Naniya ya ce Gwamna Abba ya dawo da tsarin masarauta da ya shafe sama da shekaru 700 yana aiki, inda Sarkin Kano ke zaman shugaban sauran sarakuna domin amfanin al'umma.

Gwamna Abba Kabir.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Sarki Sanusi II ya jinjinawa Gwamna Abba

Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne shugaban majalisar, ya bayyana cewa farfado da majalisar sarakuna ya zo a kan lokaci kuma ya yi daidai da tsarin tarihi da al’ada.

Ya yaba wa Abba bisa gagarumin aikin ci gaba da yake aiwatarwa, tare da tabbatar da cewa sarakuna za su yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da inganta zaman lafiya da walwalar Kano.

Yadda Sanusi II ya waiwayi tarihin Kano

A baya, kun ji labarin cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi masu kokarin rusa tarihin Kano da su yi wa kansu gyadar dogao, su hakurada shirinsu.

Sarki Sanusi II ya bayyana cewa babu wanda zai iya lalata tarihi da al'adun Kano wadanda aka gina bisa jajircewa da gaskiya.

Kara karanta wannan

Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara

Muhammadu Sanusi II ya ce idan ana maganar tarihin Kano, to ya samo asali ne daga ginshiƙan ilimi, addini, da kasuwanci da suka kafa tushe mai ƙarfi ga Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262