Abubuwan da Najeriya ke Tattaunawa da Amurka kan Barazanar Kawo Hari
- Gwamnatin Najeriya na ci gaba da tattaunawa da Amurka kan barazanar Shugaba Donald Trump na kawo farmaki kasar
- Trump ya ce ya ba ma'aikatar tsaron Amurka umarnin shirya kai hari Najeriya idan har gwamnati ta gaza kawo karshen kisan kiristoci
- Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya bayyana abubuwan da tattaunawar ta kunsa tsakanin kasar da Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Najeriya da kasar Amurka bayan barazanar Shugaba Donald Trump ta kawo farmaki kasar.
Idan ba ku manta ba, Shugaba Trump ya sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da ake zargin ana tauye 'yancin addini.

Source: Twitter
Barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa bayan haka, Trump ya kuma yi barazanar cewa da yiwuwar sojojin Amurka su kawo farmaki Najeriya domin yaki da yan ta'adda.

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Amurka ba za ta zuba ido tana kallo ana yi wa kiristoci kisan kare dangi ba a Najeriya, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance lamarin.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta wannan zargin, tana mai tabbatar da cewa matsalar tsaron kasar ya shafi kowane dan kasa.
Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka
Gwamnatin ta kuma kara da cewa Najeriya kasa ce mai bin tafarkin dimokuradiyya, wanda ya ba kowa yancin addini da kuma zaman lafiya tsakanin mabiya addinai.
Bayan haka kuma Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka domin warware sabani da rashin fahimtar ainihin abubuwan da ke faruwa a kasar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya jaddada cewa su na ci gaba da tattaunawa kan gwamnatin Amurka kan batutuwan da suka shafi tsaro.
Abin da kasashen 2 ke tattaunawa a kai
Jaridar News24 ta ce a wata tattaunawa da aka yi da shi a Abuja yau Litinin, 17 ga watan Nuwamba, 2025, Yusuf Tuggar ya ce:

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Amurka, an ji halin da ake ciki
"Abin da muke tattaunawa shi ne yadda za mu yi aiki tare wajen fuskantar kalubalen tsaro domin amfanin duniya gaba ɗaya.”
Tun a farko, Trump ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta tsara yiwuwar kai hari a Najeriya saboda, a cewarsa, “masu tsattsauran ra'ayin Islama na kashe Kiristoci.”

Source: Getty Images
Amurka za ta kawo farmaki Najeriya?
Da aka tambayi ministan ko yana ganin Amurka za ta kai harin soji, sai ya ce:
“A’a, ba na tunanin haka, saboda muna ci gaba da tattaunawa, kuma kamar yadda na fada, ana samun ci gaba, mun wuce wannan matakin.”
Najeriya dai na fama da rikice-rikice da dama, ciki har da tashe-tashen hankulan ’yan jihadi, waɗanda ke kashe Musulmi da Kiristoci ba tare da bambanci ba.
Kasae Amurka za ta fara bincike kan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa majalisar wakilan Amurka ta sanar da shirinta na gudanar da wani zama na musamman a ranar 20, Nuwamba, 2025 a kan Najeriya.
Majalisar za ta yi zaman ne domin nazari kan sababbin zarge-zargen kisan gilla da cin zarafin kiristoci da Shugaba Trump ya yi wa Najeriya.
Hakan ya biyo bayan matakin Shugaba Donald Trump na sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take hakkokin addini (CPC).
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
