Babbar Magana: An Kashe Mataimakin Shugaban APC, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kisan mataimakin shugaban APC na karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta, Ese Idisi
- Rahoto ya nuna cewa wasu mahara ne suka kashe jigon jam'iyyar APC yayin da suka kai hari kauyen Okpara ranar Asabar da ta gabata
- Jam'iyyar APC reshen jihar Delta ta yi Allah wadai da lamarin, ta kuma bukaci jami'an tsaro su binciko duk wani mai hannu a kisan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun hallaka mataimakin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta, Mista Ese Idisi.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun hallaka babban jigon APC ne a lokacin da suka farmake shi a jihar Delta da ke Kudancin Najeriya ranar Asabar da ta gabata.

Source: Twitter
Matakin da 'yan sanda suka dauka
Jaridar Punch ta tattaro cewa rundunar yan sanda reshen jihar Delta ta tabbatar da kisan Mista Idisi a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a, SP Bright Edafe ya fitar yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce duk da cewa duk da babu cikakkun bayanai a yanzu, amma rundunar ta samu tabbacin kashe Idisi a Okpara, wani kauye da ke cikin karamar hukumar.
SP Edafe ya ce:
“Mun karɓi rahoton cewa an kashe shi, kuma yanzu haka mun fara gudanar da bincike.”
APC ta yi Allah-wadai da kisan
APC ta jihar Delta ta bayyana alhini da takaicin wannan kisa mai muni, tana mai Allah-wadai da lamarin a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Mr. Valentine Onojeghuo, ya fitar.
A sanarwar, jam’iyyar APC ta bukaci ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi, ba tare da son rai ba don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Haka kuma, APC ta nemi a binciko wadanda suka dauki nauyi, da duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika, "Dole ne a kamo su tare da gurfanar da su a gaban shari’a ba tare da bata lokaci ba.”

Source: Twitter
APC ta mika sakon ta'aziyya
Jam’iyyar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan mamacin, tana mai cewa rashin Idisi babban gibi ne ga iyalinsa, al’umma, da kuma jam’iyyar APC musamman a mazabar Ethiope ta Gabas 4.
Ta bayyana shi a matsayin mamba nagari, mai biyayya, jajirtacce kuma abin dogaro wanda ya bayar da gudummawa sosai ga cigaban jam’iyyar APC a Ethiope ta Gabas.
"Rasuwarsa ba kawai rashin jigo ba ce, babban rauni ne da ya jefa mu cikin baƙin ciki," in ji APC.
Mahara sun harbe 'dan APC a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe jigon APC a jihar Zamfara, Hon. Umar S. Fada Moriki a kan hanyar Tsafe.
Marigayin ya shahara wajen kokarin kamanta gaskiya a ayyukansa, musamman kokarinsa na ganin yankin Shinkafi da Zurmi sun samu ci gaba cikin kwanciyar hankali.
Wannan na zuwa ne yayin da rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da ta'azzara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

