Yadda Ƴan Ta'adda Suka Afka wa Mazauna Zamfara, Sun Kwashe sama da Mutum 60
- ’Yan bindiga sun ƙara dura a kan al'ummomin da dama a sassa daban-daban na jihar Zamfara a ƙarshen makon jiya
- A wannan karon, sun farmaki jama'a tare da jawo asarar rayuka a kauyen Fegin Baza da ke karamar hukumar Tsafe
- Bayan kusan gilla da suka yi wa mutanen da ba su aikata laifin komai ba, sun yi garkuwa da mutane da dama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara–Mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wasu ’yan bindiga suka kai gagarumin hari a kauyen Fegin Baza na karamar hukumar Tsafe, Jihar Zamfara.
A yayin harin da aka kai a ranar Asabar, ƴan bindigan sun yi garkuwa da akalla mutum 64, ciki har da mata da ƙananan yara.

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya

Source: Facebook
Shaidu sun shaida wa Daily Trust cewa ’yan bindiga fiye da 30 ne suka bullo a kan manyan babura, suka bude wuta kan motoci da mazauna yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi barna a jihar Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane hudu sun jikkata yayin da bindiga suka buɗe masu wuta, inda aka garzaya da su Asibitin Tsafe.
Daga cikin wanda aka kashe har da jigon jam’iyyar APC, Umaru Moriki, wanda shine Sarkin Fadan Moriki.

Source: Facebook
An harbe shi ne a kusa da kauyen Fegin yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna kwana guda bayan ya halarci taron APC a Zamfara.
An gudanar da taron a gidan karamin Ministan tsaron ƙasar nan, kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Mohammed Matawalle.
Yadda aka kai hari Zamfara – Shaidu
Wani wanda ya tsira daga harin, Abdulrahman Ahmad Dole, ya ce ’yan bindigan sun tare hanyar Gusau–Funtua mintuna kaɗan bayan motar kwamishinan ’yan sandan jihar ta wuce.
Ya ce:
“Motarmu tana gaban jerin motar CP. Bayan sun wuce mu kaɗan sai muka shiga tsakiyar ’yan bindiga. Na bude ƙofa na gudu cikin daji. Sun bi ni da babura suna harbi, amma na fake a wata makaranta har sojoji suka tsince ni.”
A cewar mazauna yankin, kauyen Fegin Baza ya samu bayanan sirri cewa za a kai musu hari tun ranar Alhamis, inda suka shafe daren Juma’a suna sintiri tare da ’yan banga.
Wani mazaunin kauyen, Malam Musa Yusuf, ya tabbatar da cewa an sace mutane da dama amma an saki wasu biyu daga cikinsu su bayan an biya ƙudin fansa N500,000.
An kai karar gwamnan Zamfara ga Amurka
A baya, mun wallafa cewa wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Concerned Nigerians for Human Security ta kalubalanci Gwamna Dauda Lawal Dare kan matsalolin tsaro a jihar.
A cikin wata budaddiyar wasiƙar da ta aikawa shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, ƙungiyar ta roƙe shi da ya sanya idanu kan halin da ake ciki a Zamfara da wasu sassan Arewa.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa dubunnan mutane— daga ciki har da mata da ƙananan yara—sun mutu ko an sace su tun bayan da ‘yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna na ƙauyuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

