'Yan Kasuwa Sun Karya Farashi, Ana Sayar da Kayan Abinci da Araha a Jihar Benue

'Yan Kasuwa Sun Karya Farashi, Ana Sayar da Kayan Abinci da Araha a Jihar Benue

  • An samu faduwar farashin kayan abinci a kasuwannin jihar Benue, musamman wake, shinkafa dawa, da sauran hatsi
  • Rahoto ya nuna cewa yanzu mutane na sayen mudun wake a kan N1,500, sabanin N2,300 da aka sayar da shi a shekarar 2024
  • Sai dai a hannu daya, 'yan kasuwa sun koka cewa saukar farashin kayan ta jawo masu asara, kuma abin ya shafi manoma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Jama'an gari a Benue sun cika da farin ciki yayin da farashin kayan abinci ya karye sosai a kasuwanni, musamman a Makurdi, babban birnin jihar.

A hirar da suka yi da manema labarai ranar Lahadi, masu sayayyar kayan abinci sun ce raguwar ta taimaka matuka wajen samun saukin gudanar da harkokin gida.

'Yan kasuwa sun koka yayin da aka samu saukar farashin kayan abinci a Benue.
Wani matashi a cikin shagonsa yana sayar da kayan abinci. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

“Farashin wake, shinkafa ya ragu” — Masu sayayya

Kara karanta wannan

Da gaske an yi yunkurin kashe Laftanal Yerima a Abuja? An ji ta bakin 'yan sanda

Wata mata, Victoria Ogwuche, ta shaida wa hukumar NAN cewa, yanzu tana iya saye mudun wake a kan N1,500, sabanin N2,300 da ake sayarwa a 2024.

Ta kara da cewa tana sayen robar shinkafa (rabin buhu mai nauyin 25kg) a kan N12,000, sabanin N19,000 da take sayensa a shekarar da ta shude.

Wata kuma, Member Nyor, ta ce a 2024 yin kunu ya zama sai mai kudi saboda tsadar hatsi, amma yanzu mudun dawa ya koma N300 daga N800 da ake sayarwa a 2024 da farkon 2025.

'Yan kasuwar hatsi sun koka da asara

Onyemowo Ejeh, wata 'yar kasuwa, ta ce tana ci gaba da yin asara, domin ta sayi buhun wake mai nauyin 50kg a kan N120,000 a Disambar 2024, amma yanzu ana sayar da shi N85,000.

Ta kuma ce ta sayi buhu mai nauyin 50kg na masara a kan N85,000 a Janairun wannan shekarar, amma yanzu farashin ya karye zuwa N45,000 kacal, in ji rahoton Punch.

Game da gujjiya kuwa, ta ce:

“Na sayi buhun gujjiya kan N185,000 a Janairu, yanzu kuwa ya sauka zuwa N90,000. Ba zan iya sayar da shi a haka ba saboda asarar N95,000 a kowane buhu ta yi yawa.”

Kara karanta wannan

'Yan majalisar dokoki sun tsawaita wa'adin shugaban kasa a Benin

'Yan kasuwar Benue sun ce suna tafka asara saboda faduwar kayan abinci da aka samu.
Taswirar jihar Benue da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Arahar abinci: Masana sun gargadi gwamnati

Wani dan kasuwa, Joseph Okoh, ya ce shi ma ya sayi buhun dawa kan N70,000, amma yanzu ana sayar da shi N45,000, kuma babu masu saye saboda yawan kaya a kasuwa.

Ya kara da cewa manoma ma suna korafi saboda sun sayi kayayyakin noman su da tsada, amma yanzu karyewar kayan ya sa ba su samu ribar noman ba.

Masanin tattalin arziki, Jacob Idoko, ya ce gwamnati za ta iya jawo dorewar raguwar farashin da ake gani yanzu idan ta tallafa wa manoma da rangwamen kayan noman da suke bukata.

“Idan gwamnati ba ta tallafa wa manoma ba, babu wanda zai koma gona. Idan suka ki komawa gona, farashin kayan abinci zai nunnunka farashinsa na 2024."

- Jacob Idoko.

'Yan kasuwa sun sauke farashi a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan kasuwa a Dawanau, jihar Kano sun sanar da karya farashin kayan hatsi don ragewa al'umma radadi.

Kara karanta wannan

'Fetur zai rage kudi': IPMAN ta fadi yadda Dangote zai sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya

Shugaban kungiyar raya kasuwar Dawanau a jihar Kano, Alhaji Muttaka Isah ya ce matakin karya farashin zai kuma jawo ciniki mai yawa.

A yanzu dai farashin hatsi irin su shinkafa, wake, gero, dawa, da sauran su sun koma dai dai aljihun mutane kamar yadda Legit ta tattaro bayanai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com