Abin da Sanusi II Ya Ce game da Hare Haren ’Yan Bindiga a Kano, Ya Roki Al’umma
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuna kan yawan hare-haren yan bindiga da ke faruwa a wasu yankunan jihar
- Basaraken ya yi kira ga jama’a su ƙara tsaro, bayan karin hare-haren ’yan bindiga a ƙauyukan da ke iyaka da Katsina da ke makwabtaka da su
- Sanusi ya ziyarci Faruruwa domin jajanta wa mazauna, yana bayyana cewa gwamnati da jami’an tsaro suna ƙoƙari tare da amfani da ’yan sa-kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da hare-haren yan bindiga da ke faruwa a yankunan jihar.
Sarki Sanusi II ya ja kunnen jama’a su ƙara lura da tsaro tare da hada kai da hukumomi saboda hare-haren ’yan bindiga da suka ƙaru.

Source: Twitter
Sanusi ya ba da shawara kan yan bindiga
Yayin ziyararsa Faruruwa a Shanono, Sarkin ya jajanta wa mazauna, yana cewa tsawon watanni da suka gabata, hare-hare sun ƙaru a yankunan, cewar Aminiya.
Sanusi ya ce ya zo ne ya ƙarfafawa mutane guiwa, yana tabbatar musu cewa gwamnati da jami’an tsaro “suna yin iya bakin ƙoƙarinsu” wajen kare rayuka da dukiyoyin al'mmar yankin.
Basaraken ya koka game da hare-haren da ake kaiwa wasu yankunan da ke jihar musamman masu makwabtaka da Katsina wacce ta yi kaurin suna kan rashin tsaro.
“Tsawon watanni da suka wuce, hare-haren yan bindiga sun ƙaru a ƙauyukan da ke kusa da Jihar Katsina, inda mahara ke zuwa su sace dabbobi, su hallaka jama’a, sannan su sace maza da mata."
- Sanusi II

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya

Source: Twitter
Sanusi ya fadi kokarin gwamnati kan tsaro
Sarkin ya bayyana cewa gwamnati ta tura jami’an tsaro da sababbin kayayyaki, yana mai cewa “mutane na gani da idonsu yadda sojoji ke sintiri”.
Ya ƙara karfafa aikin ’yan sa-kai, yana gargadin maƙwabtan Katsina su kula da sulhunsu da ’yan bindiga ka da ya zama barazana ga Kano.
Basaraken ya bayyana cewa nauyi ne kan shugabanni da jagororin al'umma da su tabbatar da nuna damuwa da ta'aziyya ga mutanen da irin wannan iftila'i ya faru da su.
A ƙarshe, ya yi addu’ar zaman lafiya ya dawo, yana tabbatar da cewa za su ci gaba da kokari wurin tabbatar da tsaro da hadin kan gwamnati.
“Za mu ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinmu tare da gwamnati domin tabbatar da tsaro”.
Sanusi, malaman Musulunci sun gana da ECOWAS
Mun ba ku labarin cewa Kungiyar ECOWAS tare da shugabannin addinin sun gana game da ta'addanci yayin da ake tsaka da fuskantar barazanar Donald Trump a Najeriya,
An yi ganawar tsakanin malaman Musulunci da kungiyar da Sarki Sanusi II inda suka kuduri aniyar hada kai wajen yakar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Taron ya mayar da hankali kan inganta makarantu na addini da karfafa matasa don rage daukar su cikin kungiyoyin ta’addanci da tabbatar da samar da tarbiya a tsakanin al'umma.
Asali: Legit.ng

