Falana: Babban Lauya Ya Samo Mafita ga Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Sace

Falana: Babban Lauya Ya Samo Mafita ga Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Sace

  • Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi tsokaci kan matslalar rashin tsaro
  • Femi Falana ya bayyana cewa gwamnati na nuna fifiko wajen ceto manyan mutanen da aka sace kan talakawan da suka shiga hannun masu garkuwa da mutane
  • Babban lauyan ya bada shawara ga mutanen da aka sace kuma suka biya kudin fansa kan hanyar da za su samu hakkinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fitaccen lauya mai kare hakkin ɗan adam, Femi Falana (SAN), ya bada shawara ga 'yan Najeriyan da suka biya kudin fansa ga 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Femi Falana ya shawarce su da su gurfanar da gwamnatin tarayya a kotu su nemi a mayar musu da kuɗinsu.

Falana ya ba mutanen da aka sace shawara
Babban lauya a Najeriya, Femi Falana Hoto: Femi Falana
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta kawo rahoto cewa Femi Falana ya yi wannan magana ne a wajen bude taron sabuwar shekarar shari’a ta tsangayar shari’a, jami’ar Yakubu Gowon, Abuja.

Kara karanta wannan

'Mutane da yawa sun mutu,' Tinubu ya dauki muhimmin alkawari ga al'ummar Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Falana ya bada?

Babban lauyan ya bukaci su nemi hakan ne saboda gwamnati ta kasa sauke nauyinta na kare rayukan ‘yan kasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya ce karuwar garkuwa da mutane a kasar nan wata sabuwar shaida ce ta gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, kamar yadda kundin tsarin Mulki na Najeriya ya shimfiɗa.

Hakazalika, Falana ya ce daukar matakin shari’a zai tilasta wa gwamnati ta kara kaimi wajen magance matsalar tsaro, tare da kare haƙƙin jama'a yadda ya kamata.

Falana ya zargi gwamnati da nuna bambanci wajen ceto mutanen da aka sace, inda ake gaggauta ceto alkalan kotu, ministoci ko manyan mutane idan an yi garkuwa da su, amma talakawa kuma a bar su a hannun miyagu.

“Na ce duk wanda aka yi garkuwa da shi, iyalinsa suka biya kudin fansa, suna da damar zuwa kotu su bukaci gwamnati ta biya su kudin da suka kashe."

Kara karanta wannan

Sulhu da 'yan bindiga: Sheikh Gumi ya ragargaji masu sukarsa, ya fadi nasarorin da ya samu

"Saboda kare rayuka aikin gwamnati ne. Idan aka bar rayuwarka ta shiga hadari, dole gwamnati ta biya diyya.”
“Idan aka sace alkali ko minista, gwamnati za ta tura jami’an tsaro nan da nan. Amma idan talaka ne, ana barin ‘yan uwansa su dinga yawo suna neman kuɗin fansa.”

- Femi Falana

Falana ya bukaci a kai gwamnati kara kotu
Mai rajin kare hakkin dan Adam kuma lauya a Najeriya, Femi Falana Hoto: Femi Falana
Source: Twitter

Femi Falana ya ce tun da doka matsayi daya ta dauki kowa, dole gwamnati ta dauki mataki iri daya ga dukkan ‘yan kasa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Garkuwa da mutane ya zama kasuwa

Masu nazarin tsaro sun sha gargadin cewa garkuwa da mutane ta zama harkar kasuwanci, inda ake samun dimbin riba a cikinta.

Binciken da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun biya kimanin Naira tiriliyan N2.23 a matsayin kudin fansa daga watan Mayu 2023 zuwa watan Afrilu 2024.

Aliyu Kabir ya koka kan yadda matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a kasar nan.

"Mutane suna rasa manyan kudade wajen ba masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa domin ceto 'yan uwansu."

Kara karanta wannan

'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya

"Wannan matsalar ta zama ruwan dare domin kusan ko'ina a kasar nan ana sace mutane domin neman kudin fansa."

- Femi Falana

Falana ya ba gwamnatin Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya ba gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, shawara kan batun juyin mulki.

Femi Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kasance mai fadin gaskiya ga ‘yan Najeriya dangane da rahotannin da ke yawo kan yunkurin juyin mulki da ake zargin sojoji sun shirya.

Babban lauyan ya bayyana cewa gwamnati ba ta fito da sahihan bayanai kan rahotannin cafke wasu da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng