Barazanar Trump: Miyetti Allah Ta Roki Amurka Alfarma Kan Zargin Ta’addanci

Barazanar Trump: Miyetti Allah Ta Roki Amurka Alfarma Kan Zargin Ta’addanci

  • Kungiyar Miyetti Allah ta yi martan ga Shugaban kasar Amurka, Donald Trump kan alakanta su da ta'addanci a Najeriya
  • Kungiyar ta ce ana yi mata mummunar fahimta, tana nan a matsayin ƙungiyar kiwo mai zaman lafiya da ke fuskantar hare-hare
  • MACBAN ta bayyana cewa dubban makiyaya sun mutu ko an raba su da muhallansu, tana kuma neman Amurka ta tallafa wajen samar da mafita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta yi martani bayan zarginta da ta'addanci.

Kungiyar ta roƙi Shugaban Amurka, Donald Trump, da 'yan majalisar dokokin ƙasar su cire duk wani ambato da ke haɗa ta da ayyukan ta’addanci ko tsattsauran ra’ayi.

Miyetti Allah ta roki Trump ya bar hada su da ta'addanci
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Miyetti Allah ta tura sako ga Trump

Shugaban ƙungiyar, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Mata 6 da suka sha ƙasa a zaben gwamna a zaɓukan Najeriya

MACBAN ta ce ƙungiya ce mai zaman lafiya, ta al’ada da tattalin arziki, wadda take da niyyar ci gaban ƙasa da warware rikice-rikice tsakanin al’ummomi.

Ngelzarma ya ce kudirin ya ƙunshi bayanai da suka nuna MACBAN a matsayin ƙungiya mai makami ko ta’addanci, yana mai cewa wannan ya saba wa gaskiya, kuma yana iya lalata kokarin wanzar da zaman lafiya.

Ya bayyana cewa “Miyetti Allah” na nufin “Muna gode wa Allah” a Fulfulde, suna da ke nuna ladabi, godiya da zaman lafiya, abubuwan da ƙungiyar ta bi tsawon shekaru 40.

Ngelzarma ya ce MACBAN ba ƙungiyar addini ba ce, ba siyasa ba, kuma ba ƙungiya mai dauke da makamai ba ce.

Ya ce ƙungiya ce ta masu kiwo da aka yi rijista da ita bisa doka a Najeriya, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da tallafa wa tattalin arzikin karkara.

Miyetti Allah ta wanke kanta kan zargin ta'addanci
Kungiyar Miyetti Allah yayin taronta a Abuja da Donald Trump. Hoto: Donald J Trump, Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria.
Source: Facebook

Miyetti Allah ta fadi yadda ake kashe mambobinsu

Kara karanta wannan

AU ta mayar da martani ga Trump kan ikirarin ana kisan Kiristoci a Najeriya

MACBAN ta ce makiyaya su ne mafi yawan wadanda rikice-rikicen ƙasa suka fi shafa, tana zargin cewa dubban su sun mutu ko an kora su daga muhallansu.

A cewar bayanan ƙungiyar, daga 2015 zuwa 2025, sama da 18,640 makiyaya sun mutu, fiye da 1.29 miliyan sun rasa muhallansu, an ƙone gidaje 87,543 kuma sama da milion 1.1 na shanu an sace ko an kashe.

Ƙungiyar ta kuma lissafa wasu shugabanninta da aka kashe ko suka ɓace, ciki har da shugabannin jihohi na Nasarawa, Katsina, Kwara da Kogi.

Biyu daga cikin manyan shugabanninta, Muhammad Adamu da Injiniya Munnir Atiku Lamido har yanzu ba a san inda suke tun 2023 ba.

Ngelzarma ya jaddada cewa a daina amfani da laifin wasu miyagun mutane don a yi wa dukan makiyaya ko wani jinsi bakar magana.

MACBAN ta bukaci Amurka ta saurari bayanan da suka dogara da hujja, ta kuma tallafa wajen samar da mafita mai ɗorewa kamar farfado da gonakin kiwo, gyaran filayen kiwo, samar da ruwa da kula da lafiyar dabbobi.

Kisan Kiristoci: An taso Miyetti Allah a gaba

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da suka jawo ake kashe bayin Allah a Neja da jihohin Arewa 5

Kun ji cewa Majalisar Dokokin Amurka ta fara daukar matakai da ke nuna goyon bayan ga Shugaban kasar, Donald J Trump bayan kalamansa a kan Najeriya.

Donald Trump ya yi zargin cewa ana yiwa kiristocin Najeriya kisan kare dangi, saboda haka kasarsa ba za ta zuba ido ba.

Trump ya fara da daukar matakin sanya Najeriya a matsayin kasashen da ake samun damuwa a kansu a kan kisan kiyashin Kiristoci a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.