'Mutane da Yawa Sun Mutu,' Tinubu Ya Dauki Muhimmin Alkawari ga Al'ummar Filato
- Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnati za ta dauki matakai masu masu karfi domin dakile kashe-kashen da ake yi a Plateau
- Ya bayyana hakan en a lokacin da daruruwan ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa suka koma APC a filin taro na Jos Polo Ground
- Shugaban kasar, wanda ya yi magana ta bakin Godswill Akpabio ya ce ba zai zura ido a ci gaba da kashe mutane a jihar ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa da jama’ar Plateau cewa gwamnatin tarayya za ta kawo karshen kashe kashen da ake yi a jihar.
Tinubu ya ce gwanatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen rikice-rikicen da ake fama da su, wadanda ke haddasa kashe mutane da raba su da muhallansu.

Kara karanta wannan
Akpabio: Shugaban majalisar dattawa ya fadi halin da yake shiga kan kashe kashe a Najeriya

Source: Twitter
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana hakan a madadin shugaban kasa a taron siyasa da aka gudanar a Jos ranar Asabar, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba mu yarda da zubar da jini ba” — Tinubu
Ya ce gwamnatin tarayya na matukar damuwa da yawan hare-hare da kuma rasa rayuka da ake yi a wasu yankunan jihar.
Akpabio ya ce:
“Ina tabbatar wa jama’ar Plateau cewa an ji koke-kokenku. Plateau na neman zaman lafiya; ba kwa son ganin ’ya’yanku suna mutuwa tun suna kanana.
“Mutane da yawa sun mutu a Plateau, kuma ba ma farin ciki da hakan; shugaban kasa ma ba ya farin da hakan.
"Ba za mu musanta cewa an kashe mutane da dama ba, ko an raba wasu da gidajensu ba. Dole mu dakatar da wannan. Dole mu dawo da zaman lafiya.”
An sha kai hare-hare musamman a Bokkos da Bassa cikin wannan shekara, inda mutane da dama suka mutu, aka kone gidaje, aka tilasta wasu yin hijira daga garuruwansu.
Zanga-zanga a Jos, da batun “kisan kare dangi”
Kungiyoyi sun yi zanga-zanga a Jos suna kiran hare-haren da ake yi da “kisan kare dangi,” inda suka rika neman karin matakai daga gwamnatin tarayya.
Sai dai gwamnatin tarayya da Kungiyar Tarayyar Afirka sun yi kashedi kan amfani da wannan kalma, cewa rikicin ya ta’allaka ne kan rikice-rikicen fili, 'yan ta'adda, da rikicin manoma da makiyaya — ba wai kisan kare dangi ba.
Muhawarar ta karu ne bayan Donald Trump ya yi ikirarin cewa ana “kashe Kiristoci a Najeriya,” inda har ya yi barazanar daukar matakin soja idan ba a daina ba.

Source: Original
Filato: An samu masu sauya sheka zuwa APC
Lokacin da aka karɓi sababbin ’yan siyasa da suka sauya sheƙa, tsohon Darakta-Janar na yakin neman zaben Mutfwang, Latep Dabang, ya ce sauya shekarsu na nuni da rashin gamsuwa da yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da al’amura.
Ya ce:
“Mun yi muku alkawari ba za mu kunyata ku ba. Za mu tabbatar da cewa Plateau gaba ɗaya ta koma APC.”
Jakadiyar zaman lafiya ta isa Filato
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya tura Dr. Abiodun Essiet zuwa Plateau domin jagorantar tattaunawar zaman lafiya.
Dr. Essiet ta gudanar da tarurruka a Barkin Ladi da Jos, inda ta gana da shugabannin addini, sarakuna da kungiyoyin matasa.
An samu gagarumin ci gaba lokacin da aka warware rikicin da ya faru tsakanin manomi David Toma da wasu makiyaya da kuma sauran rigingimu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

