Matawalle Ya ba Iyalan Jigon APC da Yan Bindiga Suka Kashe Gudunmawar Miliyoyi

Matawalle Ya ba Iyalan Jigon APC da Yan Bindiga Suka Kashe Gudunmawar Miliyoyi

  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ziyarci dangin marigayi Umar S. Fada a Gusau da yan bindiga suka hallaka
  • Matawalle ya ziyarci iyalan ne inda ya mika ta’aziyya tare da bayar da tallafin miliyoyin kudi da kayayyaki
  • Sanarwar APC ta bayyana cewa marigayi Fada mutum ne nagari mai gaskiya da taimako, kuma rasuwarsa babban rashi ne ga jihar da ƙasa baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Karamin ministan tsaron ƙasa, Bello Matawalle ya ziyarci iyalan marigayi Umar S. Fada a Zamfara.

Matawalle ya mika ta’aziyya tare da bayar da tallafin Naira miliyan 10 da kuma kayayyaki ga iyalan marigayin.

Matawalle ya ziyarci gidan iyalan marigayi jigon APC
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Dr.Bello Matawalle.
Source: Original

Sanarwar da APC ta fitar a Gusau ta bayyana cewa an kashe marigayin ne sakamakon harin miyagun ‘yan bindiga, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bayan kashe kashen mutane, Tinubu ya tura jakadiyar wanzar da zaman lafiya Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka hallaka jigon APC a Zamfara

Hakan ya biyo bayan hallaka jigon APC yayin da rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ke kara kamari.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a kan hanyar Tsafe, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.

An bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mutum mai kishin yankin da cewa rasuwarsa babban gibi ce ga jama’ar Shinkafi.

An hallaka jigon APC a Zamfara
Tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara. Hoto: Murtala Bello Sokoto.
Source: Facebook

Ziyarar da Matawalle ya kai gidan jigon APC

Sanarwar ta ce ministan ya ziyarci gidansa a 'Federal Low Cost', yana mai bayyana rasuwar Fada a matsayin babban rashi ga jihar da ƙasar baki ɗaya.

Ta kuma ce marigayin mutum ne mai gaskiya, haƙuri da riƙon amana a harkokin siyasa da kasuwanci, wanda ya taimaka wa mutane da dama a rayuwa.

Ministan ya yi addu’ar Allah ya ba shi Jannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa ƙarfin gwiwa su jure wannan babban rashi da ya auku.

Kara karanta wannan

Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara

Tallafin miliyoyin kudi da Matawalle ya bayar

Sanarwar ta ƙara bayyana cewa ministan ya miƙa tallafin miliyan 10, buhunan shinkafa 50, masara 20 da biyar, da gero har buhuna 25.

Ya kuma tabbatar wa iyalan cewa gwamnati da shi kansa za su ci gaba da kulawa da su tare da tabbatar da rayuwarsu ta ci gaba cikin kwanciyar hankali.

Da yake magana da sunan iyalan, Ambasada Abubakar Hussaini Moriki ya yi godiya, yana cewa ministan ya soke al’amuransa domin halartar jana’izar marigayin.

Ya ce iyalan sun yaba yadda ministan ya taho daga Maradun zuwa Gusau domin jajantawa, alamar ƙauna da mutunta marigayin a wannan lokacin bakin ciki.

Turmutsu ya kashe mutum 1 a gidan Matawalle

Mun ba ku labarin cewa mutum ɗaya ya mutu, shida sun ji rauni a cunkoson jama’a da ya faru a gidan Ministan Tsaro Bello Matawalle a Gusau.

Lamarin ya faru ne yayin tarbar Matawalle da masoya suka yi, inda cunkuson ya jawo aka rika tattake mutane, har wani ya mutu wanda hakan ya tayar da hankulan mutane.

Kara karanta wannan

An bindige matashi a wajen jana'izar mahaifinsa bayan turnukewa da harbe harbe

Majiyoyi sun bayyana cewa yanzu haka an fara bincike domin gano ko akwai sakaci a wannan mummunan lamari da ya afku na takaici.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.