Gwamna Sule Ya Misalta APC da Jirgin Annabi Nuhu, Ƴan Najeriya Sun Yi Masa Raddi

Gwamna Sule Ya Misalta APC da Jirgin Annabi Nuhu, Ƴan Najeriya Sun Yi Masa Raddi

  • Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ayyana jam’iyyar APC a matsayin jirgin Annabi Nuhu, wanda zai cetoNajeriya
  • Gwamnan ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gwamnonin APC isassun kudade domin gudanar da ayyukan ci gaba
  • 'Yan Najeriya dai sun nuna rashin jin dadi da kalaman Abdullahi Sule, inda suka ce APC ba jirgin ceto ba ce a kasar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jam’iyyar APC ita ce “jirgin Annabi Nuhu” a siyasar Najeriya, wadda ta zo domin ceton ’yan ƙasa.

Ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin taron maraba da dubban masu sauya sheƙa daga jam’iyyu daban-daban zuwa APC a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce APC ce jirgin Annabi Nuhu da za ta ceto 'yan Najeriya
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule a taron majalisar zartarwar jihar. Hoto: @FaridaAAsule
Source: Twitter

A cewarsa, Shugaba Bola Tinubu ya samar wa jihohi isassun kudade domin inganta ayyukan gwamnati, lamarin da ya sa dubban ’yan siyasa ke komawa APC, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Taron siyasa: Ƴan takarar gwamna, ƴan majalisun tarayya sun sauya sheka zuwa APC

“Wanda bai shiga APC ba ya rasa jirgin ceto” — Sule

A jawabin sa, Gwamna Sule ya ce:

“APC ita ce kadai jirgin Annabi Nuhu na ceton Najeriya. Babu wani dalili ko uzuri da zai sa mu kasa zaben Shugaba Bola Ahmad Tinubu. Tinubu ya riga ya sauya komai a kasar nan saboda gyaransa da kokarinsa.”

Ya kara da cewa:

“Duk wanda ba ya cikin APC, to ya rasa jirgin Annabi Nuhu. APC ita ce jirgin; duk wanda bai shiga ba, za a bar shi. Plateau ma yanzu APC ce saboda abin da Shugaba yake yi wa mutane.”

Ya yi kira ga jama’ar jihar Nasarawa da su goyi bayan tazarcen Shugaba Tinubu da dukkan ’yan takarar APC a zaben gaba.

’Yan Najeriya sun mayar da martani masu zafi

Bayan furucin, jama’a da dama sun yi martani a shafukan sada zumunta, musamman Facebook.

FDmedia ya ce:

Kara karanta wannan

PDP ta sake rikicewa: Tsohon gwamnan Kogi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

“Yana da gaskiya. APC kamar jirgin Nuhu ce; duk wanda ya shiga ya tsira, zunubansa ma an yafe.”

Pita Odangla ya ce:

“Jirgin Nuhu an gina shi ne bisa umarnin Allah. Wane ubangiji ne ya umarci a kafa APC?”

Liberty Agbo ya rubuta:

“Jirgin Nuhu bai nutse ba, amma jirgin APC ya nutse, har yanzu ma yana nutsewa.”

Abubakar Sadiq Abubakar ya ce:

“Za ta ceci ’yan Najeriya daga me? Daga rayuwa mai kyau zuwa tsadar rayuwa, rashin tsaro, haraji marasa iyaka da alkawuran karya?”
Gwamna Abdullahi Sule ya ce APC za ta magance dukkanin matsalolin Najeriya
Gwamna Abdullahi Sule yana jawabi a wani gangamin APC a Nasarawa. Hoto: @NasarawaGovt
Source: Facebook

Nasarawa ta fara tattauna kundin tsarin APC

A gefe guda, Gwamna Sule ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da suka halarci zaman duba kundin tsarin mulkin APC su gabatar da muhimman shawarwarinsu ga kwamitin.

Ya yi jawabin ne yayin bude taron sabunta kundin tsarin APC na yankin Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, in ji rahoton The Guardian.

Gwamnan, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar kuma mamba a kwamitin duba kundin tsarin APC, ya ce wannan dama ce ga jam’iyyar domin yin gyaran da zai magance kura-kurai a tsarin cikin gida.

Kara karanta wannan

Turaki: PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyyar, ya fadi yadda zai kawo sauyi

Daruruwan 'yan adawa sun shiga APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Godswill Akpabio, shugaban APC na kasa, sun karɓi kusoshin 'yan siyasa da suka shiga APC.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da Sanata Istifanus Gyang, kusoshin PDP, NNPP, LP, da 'yan takarar gwamna.

Akpabio ya ce zuwan Prof. Nentawe a matsayin Shugaban APC na kasa zai baiwa jam'iyyar nasara a babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com