Bayan Kashe Kashen Mutane, Tinubu Ya Tura Jakadiyar Wanzar da Zaman Lafiya Filato

Bayan Kashe Kashen Mutane, Tinubu Ya Tura Jakadiyar Wanzar da Zaman Lafiya Filato

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Dr. Abiodun Essiet zuwa jihar Plateau domin jagorantar tattaunawar zaman lafiya
  • Dr. Essiet ta gudanar da tarurruka a Barkin Ladi da Jos, inda ta gana da shugabannin addini, sarakuna da kungiyoyin matasa
  • An samu gagarumin ci gaba lokacin da aka warware rikicin da ya faru tsakanin manomi David Toma da wasu makiyaya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura Dr. Abiodun Essiet a matsayin jakadiyarsa zuwa Plateau domin karfafa sulhu da dawo da zaman lafiya tsakanin al’ummomin jihar.

Dr. Essiet, ta kasance tana aiki ne a matsayin babbar mai taimakawa shugaban kasa kan huldar jama’a a yankin Arewa ta Tsakiya.

Tinubu ya tura jakadiyar wanzar da zaman lafiya a Filato, ta tattauna da shugabannin addinai
Jakadiyar da Tinubu ya tura Filato, Dr. Abiodun Essiet ta tattauna da al'umomin Filato. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wakiliyar Tinubu ta isa jihar Filato

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar 16 Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayo Onanuga ya sanar da cewa Dr. Essiet ta kwashe kwanaki biyu a jihar Filato tana gudanar da tattaunawa da shugabanni daban-daban.

"Ta gana da manyan limaman Kirista da shugabannin al’ummar Fulani Miyetti Allah, domin samar da hanyoyin fahimtar juna da karfafa zaman tare tsakanin manoma da makiyaya."

- Bayo Onanuga.

Wakiliyar Tinubu ta gana da al'umomin Jos

Ziyarar ta kai ga gudanar da taron dandalin tattaunawa a Jos, inda wakilai daga kananan hukumomi daban-daban, sarakunan gargajiya, shugabannin mata da matasa suka hallara domin tattauna hanyoyin karfafa tsarin zaman lafiya a matakin al’umma.

A Barkin Ladi, Dr. Essiet ta kai ziyara wajen Reverend Ezekiel Dachomo, shugaban Regional Church Council (RCC), inda suka tattauna rawar shugabannin addini wajen kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Sanarwar ta kuma ce"

"Dr. Essiet ta kuma yi jawabi ga wasu zawarawa tare da isar da sakon Shugaba Tinubu na sulhu da hada kan kabilu a jihar Filato."

Kara karanta wannan

Rawar da Bola Tinubu ya taka a rikicin Wike da soja, A.M Yerima

Dr. Essiet ta gana da shugabannin Fulani a Barkin Ladi domin karfafa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma, tare da tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na kara karfafa hadin kai.

An jaddada kudurin Tinubu na zaman lafiya a Filato

Daga nan ta jagoranci taron horaswa kan kafa tsarin zaman lafiya na al’umma a kananan hukumomi 17 na jihar.

Ta kuma yi ganawar sirri da al’ummar Irigwe, kungiyar Miyetti Allah, da kungiyar matasan Bassa LGA domin tattauna matakai na dorewar zaman lafiya da aikin kwamitin sulhu mai mutum 17.

Dr. Essiet ta jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar ganin an samu zaman lafiya, adalci da hadin kai a yankin Arewa ta Tsakiya.

Ta bayyana cewa tsarin zaman lafiya na garuruwa na taka muhimmiyar rawa wajen gina daɗaɗɗen zaman lafiya a matakin ƙananan hukumomi.

Dr. Essiet da Tinubu ya tura Filato ta gana da shugabannin addinai don wanzar da zaman lafiya.
Jakadiyar da Tinubu ya tura Filato, Dr. Abiodun Essiet ta tattauna da shugabannin addinai a Filato. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An samu nasarar sulhu tsakanin manomi da makiyaya

Daya daga cikin gagarumar nasarorin ziyarar ita ce warware rikicin da ya faru tsakanin manomi David Toma, mai gonar Agha a yankin Gyel na Jos ta Kudu, da wasu makiyaya.

"Toma ya kama shanu biyu bayan lalata gonarsa. A ranar 15 Nuwamba, shugaban Miyetti Allah na karamar hukumar Bassa, Alhaji Isah Yau, ya biya N500,000 a matsayin diyya ga Toma, wanda ya mayar da shanun.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da suka jawo ake kashe bayin Allah a Neja da jihohin Arewa 5

"Dukkan bangarorin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin dakile rikice-rikicen da irin su."

- In ji sanarwar Bayo Onanuga.

Kashe-kashe: An kafa sababbin dokoki a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana kaduwarsa kan kisan mata, yara da dattawa da aka yi a Zikwe da ke Bassa.

Ya sanar da sababbin dokoki da suka hada da haramta kiwo da daddare, hana jigilar shanu bayan karfe 7:00 na yamma da takaita zirga-zirgar babura.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa za a ba wadanda suka jikkata kulawar lafiya kyauta kuma an tura kayan agaji zuwa wuraren da abin ya shafa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com