Abduljabbar: Sowore Ya Fadi Abin da Ya Sa Ake Tsare da Malamin, Ya Sha Alwashi
- Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya koka kan cigaba da tsare fitaccen malamin addini a Kano bayan laifin batanci
- Ya bayyana cewa tun da dadewa ya yi niyyar kai wa malamin ziyara a kurkuku, amma hakan bai samu ba, abin da ya kira abin takaici
- Sowore ya yi kira da a kawo ƙarshen duk wani nau’in danniyar addini a Najeriya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi a mutunta ‘yancin kowa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fitaccen dan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore ya tabo batun ci gaba da tsare Malam AbdulJabbar Kabara da ake yi.
Abduljabbar na ci gaba da zama a gidan kaso ne bayan tuhumarsa da kalamai marasa dadi ga fiyayyen halitta Annabi SAW.

Source: Twitter
Sowore ya soki ci gaba da tsare Abduljabbar
Sowore ya bayyana haka ne a yau Lahadi 16 ga watan Nuwambar 2025 a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.
Dan gwagwarmayar ya ce abin takaici ne har yanzu a ce ana tsare da malamin duba da dalilin da ya sa aka daure shi a gidan gyaran hali.
Sowore ya ce ya kamata ya kai masa ziyara tun tuni a kurkuku amma hakan bai samu ba inda ya ce lamarin abin takaici ne.
Bukatar Sowore game da tsare Malam Abduljabbar
Ya bukaci kawo karshen danniya a bangaren gudanar da addini inda ya zargi cewa an hukunta Malam Abduljabbar ne saboda bambancin akide da wasu malaman Kano.
A cikin rubutunsa, Sowore ya ce:
“Yaya batun ‘yanci da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya dade haka? Ya kamata in kai masa ziyara a kurkuku tun tuni, tabbas wannan abin bakin ciki ne.
"Abin takaici ne cewa har yanzu malamin addini yana tsare saboda kawai fahimtarsa ko tafsirin da yake yi ya bambanta da na malamai da masu mulki a Jihar Kano ke tare da su.
"Lokacin kawo ƙarshen danniyar addini a Najeriya ya yi, yanzu."

Source: Facebook
Martanin wasu yan Najeriya ga Sowore
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan rubutun Sowore yayin da wasu ke nuna takaici game da yadda ake gudanar da addini a Najeriya.
Sai dai mafi yawan sun ce babu batun wariya ko danniya da kuma bambancin akida game da lamarin Abduljabbar da shi Sowore ke zargi.
Wasu ko sun ce ai idan har lamari ya wuce kotu har aka yanke hukunci to an bar maganar danniya inda suka bukaci yan Najeriya su rika mutunta bangaren shari'a.
An mayar da Abduljabbar gidan yarin Abuja
A baya, mun ba ku labarin cewa Hukumar gidajen yari ta Kano ta tabbatar da cewa ta mayar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wani gidan gyara hali a birnin tarayya.
Mai magana da yawun hukumar, Musbahu Kofar Nassarawa, ya ce matakin ya yi daidai da dokokin aiki da tsarin tsaro da hukumar ke bi.
Hukumar ta tabbatar da cewa sauya wurin ba zai shafi hakkokin shari’a, walwala da damar kare kansa ta doka ta ba Abduljabbar ba.
Asali: Legit.ng

