An Nemi Gwamnonin Jam’iyyar PDP 3 an Rasa a Babban Taron da Ake Yi a Ibadan
- Ana ci gaba da babban taron jam'iyyar PDP da ake gudanarwa a birnin Ibadan a jihar Oyo da ke Kudu maso Yamma a Najeriya
- Ana gudanar da taron ne duk da umarnin kotu na hana ta inda manyan jam'iyyar da gwamnoni suka halarta
- Sai dai akwai wasu gwamnonin jam'iyyar har guda uku da ba su samu zuwa ba yayin da wasu ake hasashen za su bar PDP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Babban taron jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da gudana yayin jiga-jiganta suka halarta wanda ake yi a jihar Oyo.
Gwamnonin Ademola Adeleke na Osun, Agbu Kefas na Taraba da Siminalayi Fubara na Rivers ba su halarci babban taron jam’iyyar PDP da ke gudana a birnin Ibadan da ke Oyo.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce tsagin Umar Damagum ya dage an gudanar da taron bisa dogaro da wani hukuncin babbar kotu da aka samu a Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ake yi gwamnonin na son komawa APC
Gwamnonin PDP uku da ake magana a kansu sun sha musa cewa sun shirya barin jam'iyyar mai adawa domin komawa APC.
An sha yada cewa dukansu suna da niyyar komawa APC domin ci gaba da hada kai da gwamnatin Bola Tinubu saboda samun ababan more rayuwa ga jihohinsu.
A kwananan nan, an yada cewa Gwamna Agbu Kefas ya gama tattaunawa da neman shawarwari domin shirin komawa APC.
Sai dai a bangarensa, Gwamna Ademola Adeleke ya musanta rahoton cewa zai bar jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC ko ADC a lokuta da dama.
Duk da hukuncin kotu, PDP tana taro a Oyo
Wannan na faruwa ne a yayin da jam’iyyar ke cikin rikici mai tsanani, duk da cewa ta dage kan ci gaba da gudanar da taron.
Hakan ya biyo bayan hukuncin kotu da ke neman hana gudanar da taron da aka shirya yi a birnin Ibadan wanda suka yi watsi da hakan
A wurin taron, an hango Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa, Caleb Muftwang na Plateau da Bala Mohammed na Bauchi.
Sauran sun hada da Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara tare da mai masaukin baki, Seyi Makinde na jihar Oyo mai masaukin baki.
Haka zalika, manyan ’yan siyasa irin su tsohon shugaban majalisar dattawa Adolphus Wabara, da tsoffin gwamnoni Udom Emmanuel, Babangida Aliyu da Ibrahim Shekarau sun halarci taron.
Wani dan PDP ya bayyana ra'ayinsa
Wakilin Hausa ya yi magana da dan PDP a Taraba wanda ya yi gaggawar dawo wa APC domin jiran gwamman jihar.
Abdulrahman Muh'd ya ce daman sun shirya tarbar Agbu Kefas kuma ta tabbata yana kan hanyarsa.
Ya ce:
"Wannan rashin ganinsa a taron ya kara tabbatar da cewa zai koma APC kawai lokaci da rana ake jira."
Sule Lamido ya fadi dalilin kai PDP kotu
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi tsokaci kan karar da ya kai jam'iyyarsa ta PDP a gaban kotu wanda ya jawo maganganu.

Kara karanta wannan
An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan
Sule Lamido ya yi bayanin cewa ba ya kai karar ba ne don yana rikici da jam'iyyar ko goyon bayan wani bangare kamar yadda wasu ke yadawa a karan kansu.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai halarci babban taron jam'iyyar PDP na kasa ba saboda hukuncin da kotu ta yanke wanda ake ganin akwai matsala.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

