Shugaban Najeriya Ya Shiga Cikin Jerin Mukaman Siyasa 20 Mafi Ƙarfi a Duniya
- Kujerar shugaban kasa a Najeriya ta shiga jerin manyan mukaman siyasa 20 mafi karfi da tasiri a bangarori daban-daban a duniya
- A wani rahoton kididdiga, an tattaro mukamai mafi karfi a duniya ciki har da shugabannin kasashe irinsu Amurka, China da kasar Rasha
- Kasashe masu tasowa kamar Najeriya sun shiga wannan jeri ne saboda rawar da suke takawa wajen samar da tsaro da inganta tattalin arziki a yankunansu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wani sabon rahoton ƙididdiga na duniya ya fitar da jerin manyan mukaman siyasa 20 masu tasiri fiye da kowane a halin da ake ciki yanzu a doron kasa.
Ana ganin wadannan mukamai guda 20, su na karfin fada a ji wajen inganta harkokin tsaro, karfin tattalin arziki da al'amuran diflomasiyya a tsakanin kasa da kasa.

Source: Twitter
Amurka da Rasha sun shiga ciki
Jaridar The Nation ta tattaro cewa jerin ya haɗa shugabannin manyan ƙasashe irin su Amurka, China, India, Jamus, da Rasha, wadanda ake ganin sun fi karfi a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika wadannan mukamai sun nuna karuwar tasirin ƙasashe masu tasowa kamar Brazil, Indonesia, da kuma Najeriya.
Haka kuma, rahoton ya sanya Tarayyar Turai (EU) a jerin, alamar cewa ikon ƙungiyar ƙasashe yana ƙaruwa sosai a wannan zamani na haɗin kai.
Jerin mukamai 20 mafi karfi a duniya
Ga jerin manyan mukaman siyasa 20 mafi ƙarfi a duniya:
1. Shugaban kasar Amurka
2. Sakataren Janar na Jam’iyyar Kwaminis ta China
3. Firaminiatan kasar India
4. Shugaban Hukumar Tarayyar Turai (EU)
5. Kansilan Jamus
6. Shugaban kasar Rasha
7. Firaministan kasar Birtaniya
8. Shugaban kasar Faransa
9. Firaministan kasar Japan
10. Sarkin kasar Saudiyya
11. Shugaban kasar Turkiyya
12. Firaministan kasar yahudaa watau Isra’ila
13. Firaministan kasar Kanada
14. Shugaban kasar Brazil
15. Magajin Garin birnin New York City da ke kasar Amurka
16. Shugaban Koriya ta Kudu
17. Shugaban kasar Indonesia
18. Firaministan kasar Italiya
19. Shugaban kasar Mexico

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya
20. Shugaban kasar Najeriya
Me yasa Najeriya ta shiga jerin?
Rahoton ya bayyana cewa matsayi na 20 da Shugaban Najeriya ya samu ya samo asali ne daga abubuwa da dama ciki har da girman tattalin arzikin Najeriya a nahiyar Afirka.

Source: Twitter
Sauran dalilan da aka duba wajen sanya Najeriya a matsayi na 20 akaai tasirinta a diflomasiyyar yanki musamman a ECOWAS da rawar da take takawa a tsaro da yaki da ta’addanci a yankin Sahel
Bugu da kari, an ruwaito cewa yawan al’ummar Najeriya da ke da matsayi na 6 mafi yawa a duniya, ya taka muhimmiyar rawa.
Majalisa ta kara wa'adin shugaban Benin
A wani labarin, kun ji cewa majalisar dokokin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta tsawaita wa'adin shugaban kasa zuwa shekaru bakwai.
Sabuwar dokar ta ayyana cewa shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin zai yi mulki na shekaru 7 kacal, kuma ana iya sabunta shi sau ɗaya tak.
Wannan gyara na zuwa ne kafin zaben shugaban kasa da za a yi a 2026 a jamhuriyar Benin, kasar da ke magana da harshen Faransanci a Yammacin Afirka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

