Sanusi II v Aminu Ado: Kwankwaso Ya Sake Taso da Batun Sarautar Kano

Sanusi II v Aminu Ado: Kwankwaso Ya Sake Taso da Batun Sarautar Kano

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan rigimar sarautar Kano
  • Kwankwaso ya bayyana halastaccen sarkin Kano wanda gwamnatin jihar Kano da al'umma suka amince da shi a wajen wani taron yaye dalibai
  • Tsohon gwamnan ya kuma koka kan matsalar 'yan bindiga da ta fara shafar wasu yankunan jihar Kano inda ya bukaci gwamnati ta dauki mataki

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sarautar Sarkin Kano.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake nanata cewa Muhammadu Sanusi II shi ne sarkin Kano guda daya tilo da al’ummar Kano da gwamnatin jihar suke girmamawa kuma suka amince da shi.

Kwankwaso ya ce Sanusi II halastaccen sarkin Kano
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @MSII_Dynasty, @KwankwasoRM
Source: Twitter

Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a ranar Asabar yayin bikin yaye dalibai karo na hudu na jami'ar Skyline University of Nigeria (SUN) da ke Kano.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya janye karar da ya kai PDP kotu? An ji magana daga bakinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk wani wanda aka nada daga waje ba tare da tsarin Kano ba, bai da wata karɓuwa a idanun jama’a da gwamnatin Kano.

Kwankwaso ya yabawa jami'ar SUN

Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023, ya yaba wa mahukuntan jami’ar kan jajircewa wajen inganta ilimi, tare da taya daliban da suka kammala karatunsu murna.

Ya yaba da cewa fiye da kashi 60 cikin 100 na daliban da suka kammala mata ne.

Tsohon gwamnan ya ja hankalin matasa maza su dage da karatu, yana gargadin cewa rashin jajircewa zai iya sa mata su yi musu nisa a muhimman fannoni na cigaban kasa.

Me Kwankwaso ya ce kan sarautar Kano?

Dangane da rikicin masarautar Kano, Kwankwaso ya ce:

“Muhammadu Sanusi II shi ne sarkin Kano guda daya da mutanen Kano da gwamnatin jihar Kano suka amince da shi.”

Kwankwaso ya koka kan rashin tsaro

A kan batun tsaro, tsohon gwamnan ya nuna damuwa kan hare-haren da wasu kungiyoyin 'yan bindiga ke kawowa daga jihar Katsina zuwa kauyukan Kano kamar Tsanyawa, Shanono, Gwarzo, da Karaye.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka zuwa jam'iyyar YPP? Gaskiya ta fito

Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki mataki cikin gaggawa don dakile barazanar.

“Idan gwamnati ta kasa kare rayuka da dukiyoyin jama’a a cikin iyakokinta, akwai bukatar wannan gwamnati ta koma ta sake nazari."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Ya ce matsalar tsaro da ta samo asali a Zamfara yanzu ta yadu ta shiga Sokoto, Kebbi, Kaduna, kuma tana barazanar shafar Kano da Jigawa.

Kwankwaso ya tuna yadda ya kashe makudan kudade wajen inganta tsaro a lokacin gwamnatinsa, yana mai kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta kara jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Najeriya.

Kwankwaso ya ba gwamnati shawara kan rashin tsaro
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A nasa bangaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne jagoran jamii'ar, ya shawarci sababbin daliban da aka yaye da su kasance masu gaskiya da hidima ga al’umma.

Ya ce ainihin kimar ilimi ba a takardar shaidar kammala karatu take ba, a irin tasirin da mutum zai yi ga al’umma ne.

Kwankwaso ya hadu da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje sun hadu tun bayan zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Manyan PDP 2 sun ja daga a kan babban taron jam'iyya na kasa

Tsofaffin gwamnonin na Kano sun hadu ne a gidan tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, da ke Abuja, inda suka je domin yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Ganduje ne ya mika wa Kwankwaso hannu yana murmushi, shi ma jagoran Kwankwasiyya ya karba ba tare da nuna alamar wata matsala a fuskarsa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng