Ba Sassauci: Sojojin Sama Sun Farmaki Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara, an Soye Miyagu
- Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan tsagerun 'yan ta'adda a wani yanki na jihar Zamfara
- Sojojin sun lalata sansanin 'yan ta'adda tare da lalata wuraren da suke ajiye kayayyakin da suke amfani da su
- A cikin sanarwar da rundunar sojojin sama ta fitar, ta bayyana cewa 'yan ta'adda da dama sun bakunci lahira sakamakon hare-haren
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta kai harin sama a kan babban sansanin ‘yan ta’adda a jihar Zamfara.
Sojojin saman sun lalata sansanin 'yan ta'addan da ke Sauri, cikin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a shafin X a ranar Asabar.
Sojojin sama sun farmaki 'yan ta'adda a Zamfara
Ehimen Ejodame ya ce bangaren sama na rundunar Operation Fansan Yanma ya kaddamar da harin a ranar Jumma'a, 14 ga watan Nuwamba, 2025.
Ya bayyana cewa hare-haren sun biyo bayan cikakken bincike da samun bayanan sirri, wanda ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda na gudanar da munanan aikace-aikace a wurin.
Hakazalika an gano suna boye shanun da suka sace a wani wuri mai tsawo da suke amfani da shi a matsayin maboyarsu da ajiyar kayan aiki.
“Dakarun sama sun kai hare-hare masu daidaito sau da dama a kan wuraren da aka gano. An yi nasarar kai hare-hare kai tsaye a wuraren, inda suka tarwatsa ‘yan ta’adda da suka yi kokarin guduwa cikin daji, daga nan aka bi sahunsu aka kuma ci gaba da murƙushe su.”
“Aikin ya yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata gine-gine da muhimman wuraren ajiye kayan aiki, wanda ya rage musu karfin gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin.”
- Air Commodore Ehimen Ejodame
Sojojin sama sun taso 'yan ta'adda a gaba
Ya kuma nakalto maganar hafsan sojojin sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, wanda ya jaddada kudirin NAF na ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda lamba, yana mai cewa:

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun ga ta kansu: Hafsan sojojin sama ya sha alwashi kan rashin tsaro
“Za mu same su, za mu bibiye su, kuma za mu kare jama’armu.”

Source: Original
NAF ta ce wannan nasara ta kara tabbatar da aniyar Operation Fansan Yanma na hana ‘yan ta’adda samun mafakar tserewa, tare da karfafa kokarin samar tsaro a Zamfara da kuma ba da gudunmawa ga yunkurin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
Nasarar abin a yaba ce
Wani mazaunin Zamfara, Jamilu Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da dakarun sojojin suka samu abin a yaba ce.
"Wannan babbar nasara ce sosai. Muna shiga cikin halin farin ciki duk lokacin da muka ji cewa jami'an tsaro sun samu nasara kan wadannan miyagun."
"Za mu ci gaba da addu'ar Allah Ya ba su nasarar kakkabe wadannan tsinannun 'yan ta'addan da suka addabi mutane."
- Jamilu Abdullahi
Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aiki samar da tsaro sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi barna bayan kashe jami'an tsaro da sace mutane kusan 50 a Neja
Dakarun sojojin sun yi musayar wuta mai tsanani da 'yan ta'addan bayan sun shirya musu kwanton bauna lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Dutsen Mandara.
Hakazalika, sojojin sun kashe dan ta'addan ISWAP guda daya tare da kwato makamai da babura a hannunsu.
Asali: Legit.ng
