'Yan Ta'adda Sun ga Ta Kansu: Hafsan Sojojin Sama Ya Sha Alwashi kan Rashin Tsaro
- Babban hafsan sojojin sama ya kai ziyarar aiki domin duba dakarun rundunar da ke aikin samar da tsaro a jihar Katsina
- Air Marshal Sunday Aneke ya karfafi gwiwar dakarun kan su ci gaba nuna rashin tausayi kan 'yan ta'addan da ke kai hare-hare
- Hakazalika, ya sha alwashin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato dukkanin yankunan da ke hannun 'yan ta'adda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Hafsan sojojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bada tabbaci kan yakin da ake yi da 'yan ta'adda.
Sunday Aneke ya tabbatar da cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ba za su sassauta ba har sai sun karɓo dukkanin wani yanki da ‘yan ta’adda ke barazana ko suka mamaye.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce ya yi wannan jawabi ne a ranar Jumma’a yayin ziyarar aiki da ya kai a sansanin dakarun sama na rundunar Operation Fansan Yanma da ke Katsina.

Kara karanta wannan
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa, an cafke hatsabibin ɗan bindiga a Kaduna
Aneke ya ba sojojin sama shawara
Aneke ya umurci dakarun NAF da su kara himma wajen cika umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kawar da duk wata barazana ga tsaron ‘yan Najeriya.
“Ba za mu sassauta ba ko na ɗan lokaci. Al’umma na kallonmu mu dawo da zaman lafiya mu kuma karɓo kowace ƙasa da ‘yan ta’adda da masu laifi suka yi barazana a kanta."
- Air Marshal Sunday Aneke
CAS ya ce yanayin tsaro a Najeriya ya zama mai matukar rikitarwa, inda miyagu marasa ji ke haddasa tashin hankali da rasa rayuka. Ya bukaci jami’an NAF su kasance masu kuzari, sababbin dabaru, kuma yin daidai a harbi, domin magance barazana.
Gwamnatin tarayya ta samu yabo
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya ta ba da goyon baya mafi girma ga NAF, ciki har da samar da sababbin jiragen sama da na’urorin zamani, karin makamai masu inganci da horaswa ta musamman ga jami’ai.
Wannan tallafi, a cewarsa, ya dora wa NAF babban nauyin kare kasa da jama’a, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
Aneke ya yabawa sojojin da ke aiki a yankin bisa jarumtaka, daidaito a aiki, duk da kalubalen da suke fuskanta, yana mai ba da tabbacin cewa za a kawar da dukkan barazanar tsaro a faɗin kasar.
“Ba za mu huta ba har sai mun kawar da duk wata barazana ga ikonmu."
“Duk inda suka buya, cikin daji, kwazazzabai ko kauyuka, za mu same su, kuma za mu kai farmaki ba tare da kuskure ba.”
“Manufarmu a bayyane take, mu bi su mu kawar da su, mu kuma kare jama’armu."
- Air Marshal Sunday Aneke

Source: Facebook
An bukaci sojoji su zage damtse
CAS ya bukaci dakarun su ci gaba da kyautata ayyukansu tare da tabbatar da cewa kowane aiki na nuna ladabi, hidima da kishin kasa, wadanda su ne ginshikan NAF.
Ya kara da cewa walwalar jami’ai ita ce fifikon rundunar, yana mai cewa ba za a yi nasarar yaki da rashin tsaro ba tare da kula da jin dadin ma’aikata ba.
“Rundunar da ke yaki dole ta rayu cikin kwanciyar hankali. A karkashin jagorancina, walwalar ku, horaswa da kayan aiki za su daidaita da jarumtarku a fagen daga."
“Ku ne garkuwar kasa, kuma tsaronku da kwarin gwiwarku abubuwa ne da ba za a yi watsi da su ba."
- Air Marshal Sunday Aneke
Sojoji sun cafke mai ba 'yan ta'adda makamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar tarwatsa ayyukan 'yan ta'adda a jihar Taraba.
Dakarun sojojin sun kama wani mutum da ake zargin mai safarar makamai ne, kuma an same shi da bindigar AK-47 da harsasai 53.
Sojojin masu aikin samar da tsaro sun kai samame ne bayan samun sahihin bayanan sirri daga mazauna yankin.
Asali: Legit.ng

