'Yan Bindiga Sun Yi Barna bayan Kashe Jami'an Tsaro da Sace Mutane kusan 50 a Neja

'Yan Bindiga Sun Yi Barna bayan Kashe Jami'an Tsaro da Sace Mutane kusan 50 a Neja

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan da ke jihar Neja a tarayyar Najeriya
  • Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutane kusan 50 a hare-haren da suka kai a kauyukan da ke karamar hukumar Mashegu
  • Hakazalika, 'yan bindigan sun kashe wasu 'yan sa-kai da suka bi sahunsu bayan sun yi awon gaba da bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Akalla ‘yan sa-kai 16 sun rasa rayukansu, yayin da aka sace mutane 42 a jerin hare-haren ‘yan bindiga a jihar Neja.

'Yan bindigan dai sun addabi al’ummomi daban-daban da ke cikin karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Neja
Babban hafsan hafsoshi da gwamnan Neja, Umar Bago Hoto: @HQNigerianArmy, @HonBago
Source: Twitter

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa hare-haren sun faru ne tsakanin Lahadi 9 ga Nuwamba da Alhamis 13 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan sanda sun ba hammata iska a Benue, an ji abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Neja

Lamarin da ya bar wasu kauyuka cike da tsoro yayin da mutane suke tsere daga matsugunansu.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce hare-haren sun fara ne a kauyen Dutsen Magaji a ranar Lahadi, inda aka yi garkuwa da mutane 22.

“Da suka zo ranar Lahadi, ‘yan sa-kai sun bi su inda suka yi musayar wuta da su. A wajen arangamar ‘yan sa-kai uku sun mutu, mutane biyar kuma yanzu haka suna asibiti."

- Wani mazaunin yankin

Ya ce maharan sun dawo da asuba ranar Alhamis 13 ga Nuwamba, suka kai hari a kauyen Magama yayin da jama’a ke cikin sallar asuba.

“Sun zagaye masallaci yayin da ake sallah suka tafi da fiye da mutane 20. ‘Yan sa-kai sun bi sahunsu ba tare da sanin an yi musu kwanton bauna ba. ‘Yan bindigan sun bude wuta, inda ‘yan sa-kai 13 suka mutu da dama suka jikkata."

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Lakurawa sun kai harin ta'addanci a Sokoto, sun yi barna mai girma

- Wani mazaunin yankin

Mahukukunta sun yi magana kan lamarin

Isah Ibrahim Bokuta, mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Mashegu, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.

Ya bayyana ‘yan sa-kan da suka mutu a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayukansu domin kare al’ummarsu.

Isah Ibrahim Bokuta ya ce karamar hukumar Mashegu na godiya ga jarumtaka da sadaukarwar da suka nuna wajen kare yankin.

A lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai tuntubi hukumomi domin tabbatar da bayanai kuma zai fitar da cikakken rahoto.

'Yan bindiga sun sace mutane da dama a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane sun bar matsunansu

A halin da ake ciki, mazauna yankin sun shaida cewa mutane da dama sun tsere daga kauyukansu tun daga ranar Litinin saboda yadda tsaro ya tabarbare.

Yanzu haka sun gudu zuwa Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu kauyuka, yayin da wasu suka koma wurin ‘yan uwa da ke nesa domin tsira.

Kara karanta wannan

ISWAP: Masu hidimar kasa, NYSC sun tsallake rijiya da baya a Borno

A cewar majiyoyi kauyukan da aka tsere daga cikinsu sun hada da: Dutsen Magaji, Borin-Aiki, Gidan Ruwa da Magama.

An yi zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga

A wani labarin kuma kun ji cewa mutanen kauyen Danjanku a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro..

Fusatattun matasa sun fito kan tituna ne domin nuna adawa da yadda 'yan bindiga ke kai musu hare-hare.

Sai dai, an samu asarar rai bayan da jami'an tsara suka yi yunkurin tarwatsa mutanen da suka fito zanga-zangar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng