Sowunmi Ya Hango Wurin da Gwamnatin Tinubu Ta Yi Kuskure a Rigimar Wike da Matashin Soja
- Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya bankado wurin da yake tunanin gwamnatin tarayya ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja
- Segun Sowunmi ya yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta tafiyar da lamarin yadda ya dace ba
- Ya kuma soki ministan Abuja, Nyesom Wike bisa rashin ladabi a mu'amala da jami'an sojoji, ya ce dole ministan ya sarrafa kansa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mai magana da yawun Atiku Abubakar, Segun Sowunmi, ya caccaki Gwamnatin Tarayya kan rigimar da ta faru tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da sojan ruwa.
Sowunmi ya bayyana cewa ko kadan gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu ba ta yi abin da ya dace kan wannan lamari ba.

Source: Twitter
Jigon PDP ya fadi haka ne yayin da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Irabor ya tsoma baki kan rigimar Wike da matashin soja a Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuskuren da gwamnatin Tinubu ta yi
Miata Sowunmi ya ce ra’ayoyin jama’a na nuna yadda ba a jin dadi da damuwa kan yadda Wike ke gudanar da harkokinsa a gwamnati.
“Idan gwamnati na sauraro koken jama'a, ina tsammanin za ta saurari abin da ake fada a rediyo, talabijin, da kuma abin da ke faruwa a soshiyal midiya.
"Abin da za su fahimta cikin sauki shi ne cewa Gwamnatin Bola Tinubu tana da matsalar Wike,” in ji Sowunmi.
Sowunmi ya bayyana tsohon gwamnan Ribas a matsayin mutum mai kuzari, ƙwarewa, da dagewa a kan aiki, amma ya ce ya kasa sarrafa gogewaraa yadda ya kamata.
Ya ce ministan ya yi kuskure wajen tunkarar matashin sojan ruwa, Latfanal A. M Yerima, inda ya zargi Wike da raina manyan shugabanni da yan surutu ta yadda kowa ya gaji da shi.
Abin da Obasanjo ya fada wa Sowunmi
Sowunmi ya kuma tuna wata shawara da ya taɓa samu daga tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo:
“Na taɓa tambayar Obasanjo yadda ake sa sojoji su mutunta gwamnati a mulkin farar hula. Sai ya ce, ‘sojoji suna da horo sosai. Ba za su karɓi umarni daga wanda suka ga bai da ɗabi’a ko basira ta shugabanci da ta dace ba."
Ya jaddada cewa ya zama dole jami’an gwamnati su nuna kwarewa da ladabi yayin mu’amala da rundunar tsaro.

Source: Facebook
“Duba yawan bidiyon barkwanci da ya fita daga cacar cakin Wike da soja, ba zai yiwu ka tafiyar da gwamnati haka ba.
"Yan Najeriya kake wa aiki, shugaban kasa kake wa aiki, bai kamata ka damu mutane da yawan surutu ba. Ya zama doke ka sarrafa kanka."
- In ji Segun Sowunmi.
Irabor ya soki ministan Abuja, Wike
A wani rahoton, kun ji cewa Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya nuna damuwa kan halayyar da ministan Abuja, Nyesom Wike ya nuna a takaddamarsa da sojan ruwa.
Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya (CDS) ya ce kalmomin da Wike ya yi amfani da su kan wanda ke sanye da kakin soja sun keta mutuncin kasar nan.
Irabor ya ƙara da cewa cin mutuncin soja da irin waɗannan kalamai da Wike ya yi amfani da su tamkar cin mutuncin ikon da shugaban ƙasa ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

