Ana Wata ga Wata: 'Yan Majalisa Sun Fara Shiri, Za Su Tsige Shugaban Majalisa a Ondo
- Rikici ya sake kunno kai a majalisar Ondo yayin da ‘yan majalisa 12 suka fara shirin tsige shugaban majalisar, Olamide Oladiji
- Masu gabatar da kudirin tsige kakakin sun bukaci EFCC ta binciki zargin da ake yi wa Oladiji na wawura Naira miliyan 50
- Rikicin ya fara ne a lokacin da gwamnan Ondo ya gabatar da karin kasafin ₦531bn, inda wasu suka fice daga zauren majalisar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Sabon rikici ya sake tashi a majalisar dokokin jihar Ondo yayin da ‘yan majalisa 12 suka fara daukar matakan tsige kakakin majalisar, Olamide Oladiji.
‘Yan majalisar sun zarge shi da aikata munanan laifuffuka, ciki har da rashawa, karkatar da kudaden jama’a da kuma karya tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Source: Facebook
Ana zargin shugaban majalisa da rashawa
Wannan shiri na kunshe ne a takardar tsige shi da suka gabatar tare da sanar da rashin amincewarsu da yadda yake gudanar da harkokin majalisar, in ji rahoton The Cable.
A cikin takardar, 'yan majalisar 12 suna mai cewa Oladiji ya zubar da mutuncin majalisar kuma ya tauye amincewar jama’a da ya rataya a wuyansa.
Masu gabatar da kudirin sun zargi kakakin majalisar da karkatar da N50m da aka ware domin gudanar da zaman sauraron jama’a.
Bugu da kari, sun ce ya wawure kudaden aiki na wata-wata da ake bai wa majalisar, lamarin da suke cewa ya sabawa ka’idodi da dokoki masu karfi.
Dokokin da shugaban majalisa ya karya
A cikin takardar tsige shi, sun zayyano dokoki da dama da aka ce Kakakin ya karya, ciki har da:
- Sakin layi na 9, jadawali na biyar na Kundin Mulki na 1999 (da aka sabunta) – wanda ya hana cin hanci da almundahana.
- Jadawali na bakwai na kundin tsarin mulki na 1999 (wanda aka sabunta) - karya alkawari da ke a rantsuwar kama aiki, da rantsuwar biyayya ga kundin
- Sashe na 19 na dokar ICPC (2000) - amfani da ofis ta haramtacciyar hanya
- Sashe na 390 na dokar laifuffuka (cap. C38, LFN 2004) - satar dukiyar jama'a a tsakanin jami'an gwamnati.
Asalin rikicin da janyo EFCC a ciki
‘Yan majalisar sun bukaci Hukumar EFCC ta gaggauta bincike da gurfanar da shugaban majalisar, tare da dawo da duk wani kudi da ake zargin an karkatar.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa 'yan majalisar sun ce wadannan miyagun ayyuka sun kai ga “tabarbarewar martaba da ayyukan doka na majalisar.”
Rikicin ya fara ne a makon da ya gabata lokacin da wasu ‘yan majalisa suka fice daga majalisar yayin tattaunawa kan karin kasafin ₦531bn da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya gabatar.
Masu adawar sun zargi shugaban majalisar da yunkurin tsallake kudirin kasafin cikin gaggawa ba tare da amsa tambayoyi kan nakasun da aka samu a kasafin 2025 ba.
‘Yan majalisar da ke neman tsige shugaban majalisa
Sun hada da:
- Jide Oguntodu (Akure ta Kudu 1)
- Temitope Akomolafe (Ifedore)
- Fatai Atere (Akoko NW 1)
- Toyin Japhet (Akoko NE)
- Raymond Daodu (Akoko SW 1)
- Samuel Ifabiyi (Odigbo 1)
- Babatunde Fasonu (Odigbo 2)
- Oluwatosin Ogunlowo (Idanre), da sauransu, inda suka kai mutum 12.
Shugabanni 2 a majalisar Ondo sun yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Ondo ta yi wasu ƴan sauye-sauye tsakanin shugabanninta a ranar Talata, 3 ga watan Yuni, 2025.
Mataimakin Kakakin majalisa, Abayomi Akinruntan, da shugaban masu rinjaye, Emmanuel Ogunmolasuyi sun miƙa takardar ajiye muƙamansu.
Shugabannin biyu sun yi murbaus ne domin mutunta yarjejeniyar raba muƙamai, ƴan Majalisa sun zaɓi mambobi biyu da za su maye gurbinsa nan take.
Asali: Legit.ng


